A kwannan an shiga wani yanayi game da irin wakilcin da ake mana a kasar nan. Wani ma’auni na nuna cewa demokuradiyyar mu bata ci gaba ba, shi ne a tsawon shekarun da muka kwashe a kan tafarkin dimokuradiyya har yanzu majalisa ba ta tabbatar wa al’umma wakilcin da ya kamata ba; talaka na nan inda yake, mutanen mazabu suna cikin wahala, amma da zarar an zabi dan majalisa sai ya koma rayuwar sheke aya. Wane irin wakilci ’yan majalisa ke yi wa al’umma ne?
Ko a kwananan wani sanata sai da ya yi halin dan bunsuru, kuma ko kunya babu ya bude baki yake cewa wai ai ko mai ya yi bai sabawa dokokin kasa ba! Wani abin bakin ciki shi ne yadda suke neman kariya ga mabarnata, watau idan dan siyasa ya yi almundahana ya tsira, amma a rika kashe barayin awaki! Ba ruwansu.
Da sun ci sai su fara kyamar wadanda suke wakilta, ba ziyara balle zumunci. Ganin ido, wannan ta zama wata dabi’a ga ’yan siyasar Najeriya, dole sai sun yaudari talakawa, amma yau da gobe sun bude mana ido. Sojojin baka inda suke daukar mutane aiki a facebook da wazzaf, irin wadannan matasa za ku ga suna neman mayar da karya gaskiya, su soki duk wanda ya fadi zahiri a matsayin dan bakin ciki. Matasa sun kashe kansu wajen zama mayakan karya, sun sadaukar da kansu don kare wasu, wani ya zama, kai ka bi, a haka za a kare a bauta, an haifi mutum da ’yanci ya mayar da kansa bawa! kirikkiri wanda ba ruwansa da mutane ya zama wakilinsu, mutanen da ba ruwansu da kowa sai duniyarsu, gidajensu sun fi na kowa kyau, ga manyan motoci, yashe za su iya wakiltar mutane, su gina musu gidaje ko su ba su motoci! Burinsu su yi nasara a duniya, idan da hali su fi kowa kudi!
Ganin abin da ake samu a majalisar tarayya ya sa mutane sun dukufa wajen ganin sai sun yi takara, kuma kowa na neman ci a kowane hali, ba don kyautatawa ba, sai dai don abin da za a samu! Idan kyautatawar ce to sai ka yi takara? Ka fara daga makusanta mana! Kun mayar da mutane jari! A haka suke aringizo a kwangilolin kasafi. Wasu ma ba su zuwa majalisar, su dai a biya su kawai, wasu sun zama kurame, ko an hasko su ba su da ra’ayi, ba su tuntubar mazabu game da dalilin da ya sa suke wakiltar jama’a. Don Allah yaushe za mu ci gaba da zama a haka?
Domin talakawan Najeriya na da saurin ganewa, yau da gobe sun sa matasa sun gano ‘yan majalisa na yi wa wannan gwamnatin bita da kulli, an gaza komai, ko kasafin an kasa aiwatar da shi, sai ka-ce na-ce!
Ko wane kokari suke wajen ganin an zamanantar da ilimin boko a kasar nan, ko haramta bara a tarayyar Najeriya, ko yaki da talauci, kuma abin da za su yi ke nan su samu kima a idon talakawa.
Mene ne suka yi da aka janye tallafin man fetur, su wa suka yaki karin kudin aikin hajji, ko janye tallafin taki, ko koma bayan ilimi da kiwon lafiya? Wani abu da ke jawo matsala a majalisa, shi ne, yadda tsofaffin gwamnoni ke neman kujerun sanatoci kafin wa’adinsu ya kare a haka sai su nemi yadda za su kare kansu bayan sun tube rigar kariyar gwamna.
Lokacin da ake neman kudi da kujerar wakilci ya wuce, mutane na kallon lokacin da aka rantsar da wakili da yadda ya tafiyar da lamuran mazaba. Mun gane yawan surutu dabi’ar makaryata ce. Ba su jin maganar iyayen jam’iyya, hasali ma iyayen jam’iyyar da ita kanta jam’iyyar sun jefa ta aljihunsu.
Ya kamata wakilanmu su rika kawo kudurori a majalisa don kare hakkin talakawan da suke wakilta. Ba wai a buge da wasu bukatu ba da hankali ba zai dauka ba. Kamar yadda suke neman kariya ga barayin gwamnati, wanda hakkan ya tabbatar da suna da abokai ko wasu da suka zama gwamnoni suka fada majalisa da neman kariya kan kudin da suka sace. Ko me ya sa kusan kowane gwamna bayan ya gama zango biyu sai ya ce shi sanata yake nema? Bayan ba a gamsu da gwamnan da ya yi ba. Su kansu iyaye a jam’iyu ya kamata su rika tsawata wa wadanda ba su cancanta ba, don hakan zai rage tasirin ubangidanci a siyasar Najeriya.
A hankali an fara yin kiranye, sannan a wasu yankunan sanatoci ba su isa su kai ziyara inda suke wakilta ba, sai da shirin yakar mazabar idan ya kama! To wai don Allah wani irin mulki ne wannan?
A fahimtata idan ana son a gyara alakar mutane da wakilansu, dole talakawa su guji tasirin kudi, kuma idan mutum ya saba a saba masa, ba wai sai an jira shekaru hudu ba. Sannan su kansu sarakuna da jami’o’in kasar nan su bar karramawa da nada mabarnata. Ya kamata ko kyautar gurbatattun wakilai ta haramta garemu.
kuma wani mataki shi ne a sa dokar idan gwamna ya gama wa’adinsa a ba da damar bincikensa kafin ya tsaya takarar sanata ya wakilci jama’a. Tabbas kifi na ganinka mai jar koma. Mutane ba za su manta ba, kowa a sane yake kan cewa an shiga jam’iyyar Buhari an kai labari, kuma muna son a gane cewa ‘kunnen jaki ba kaho ba ne!’
Tabbas hakuri ya fara kare wa mutanen tarayyar Najeriya, musamman talakawa. Domin abubuwa sai kara cabewa suke yi, ba jam’iyya ba, ba wakilin ba. A zabo daga cikin talakawa, kar wani ya lakuta mana zuma abaki da ya samu dama ya harbe mu da kari, tabbas zabe na zuwa.
Buhari Daure +2347035986444 Muryar Talaka Modoji, Katsina Buhari Daure [email protected].