✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wanda ya jagoranci sace Daliban Kankara ya mika wuya

Mutum da ya jagoranci sace dalibai 344 ya rungumi shirin afuwar gwamnati

Shugaban ’yan bindiga da suka yi garkuwa da daliban Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke garin Kankara a Jihar Katsina ya mika wuya ga gwamnati.

Mutum da ya jagoranci sace dalibai 344 da gungun ’yan bindigar suka yi a makarantar ya mika wuya ne tare da wasu yaransa ga shirin afuwa na Gwamnatin Jihar Zamfara.

Hukumomi sun ce Auwalun Daudawa ya mika wuya ne a ranar Litinin, inda suka mika wuya sun kuma mika bindiga kirar AK-47 guda 28 ga Gwamnatin Jihar Zamfara.

Auwalu da yaran nasa sun mika wuya ne kimanin wata biyu bayan gungun da yake jagoranta sun sace daliban, wanda ya tayar da kura matuka a fadin duniya.

A lokacin, sun yi awon gaba da daliban ne awanni kadan bayan saukar Shugaba Muhamamdu Buhari a Jihar Katsina, kuma sai da aka yi kwanaki biyar kafin su saki daliban.

Makaman da Auwalu da yaransa suka mika wa Gwamnatin Jihar Zamfara.

Kimanin kwanaki 10 kafin nan wasu ’yan bindiga shida suka tuba tare da mika wa hukumomin Jihar bindigogi 14 suna masu alkawarin watsar da ayyukan ’yan bindiga da sauran ababe na ta’adda.

Wadanda aka karbi tubansu a fadar Gwamnatin Jihar da ke birnin Gusau, sun yi rantsuwa da Alkur’ani cewa ba za su sake komawa wannan mummunar ta’ada ba.

Kazalika, jagoransu Auwalu Daudawa ya yi alkawarin janyo ra’ayin wadanda har yanzu suke rike da makamai domin su tuba.

Da yake karbar mutanen da suka tuba, Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya kirayi dukkan ’yan bindigar da su fito su amince da tsarin sulhu da gwamnatinsa ta kirkiro inda ya yi alkawarin kula da duk wadanda suka tuba.

“Gwamnatina za ta kula da duk ’yan bindigar da suka tuba sannan zan ci gaba da tattaunawa da su domin kawo karshen ta’addanci a Jihar,” inji Matawalle.

Matawalle ya yi kira ga mutanen jihar, musaman ’yan siyasa da su bai wa gwamnatinsa goyon baya a kokarinta na kawar da masu satar mutane da sauran ababe na ta’ada.