✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wanda ake zargi da kashe Shugaban APC na Jihar Nasarawa ya shiga hannu

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana nasarar cafke mutumin da ya kashe shugaban APC a jihar.

‘Yan sanda a jihar Nasarawa sun cafke mutumin da ake zargi da kashe shugaban jam’iyyar APC a jihar, Mista Philip Tatari Shekwo.

Gwamnan jihar, Abdullahi Sule ne ya bayyana hakan yayi wani taro da aka yi a fadar gwamnatin jihar da ke Lafiya a ranar Talata.

Gwamnan ya ce, “Wanda ake zargin mai suna Mohammed Usman, gagarumin dan ta’adda ne, ‘yan sanda sun yi nasarar cafke shi.

“Bayan gudanar da bincike ya tabbatar da cewa shi ne ya halaka shugaban APC, Mista Philip Tatari Shekwo,” in ji gwamnan.

Idan za a iya tunawa dai a kwanakin baya ne gwamnan jihar ya bayyana cewa jami’an tsaron jihar sun kama mutane tara da ake zargin suna da hannu a kisan shugaban na APC.

An kashe Shekwo ne har lahira kwana daya da yin garkuwa da shi a gidansa, kafin daga bisani kuma a tsinci gawarsa.