‘Yan sanda a jihar Nasarawa sun cafke mutumin da ake zargi da kashe shugaban jam’iyyar APC a jihar, Mista Philip Tatari Shekwo.
Gwamnan jihar, Abdullahi Sule ne ya bayyana hakan yayi wani taro da aka yi a fadar gwamnatin jihar da ke Lafiya a ranar Talata.
- An sace Shugaban APC na Jihar Nasarawa
- An tsinci gawar shugaban APC na jihar Nasarawa jim kadan da sace shi
- Buhari ya yi Allah-wadai da kisan shugaban APC na jihar Nasarawa
- Mutum 9 sun shiga hannu kan kisan Shugaban APC na Nasarawa
Gwamnan ya ce, “Wanda ake zargin mai suna Mohammed Usman, gagarumin dan ta’adda ne, ‘yan sanda sun yi nasarar cafke shi.
“Bayan gudanar da bincike ya tabbatar da cewa shi ne ya halaka shugaban APC, Mista Philip Tatari Shekwo,” in ji gwamnan.
Idan za a iya tunawa dai a kwanakin baya ne gwamnan jihar ya bayyana cewa jami’an tsaron jihar sun kama mutane tara da ake zargin suna da hannu a kisan shugaban na APC.
An kashe Shekwo ne har lahira kwana daya da yin garkuwa da shi a gidansa, kafin daga bisani kuma a tsinci gawarsa.