✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wanda ake tuhuma da kisa ya bukaci alkalin kotun ya daura aurensa

Ya roki alkalin da ke sauraron shari'ar zargin shi da kisa ya daura masa aure.

Wani mutum da aka gurfanar a gaban kotu kan zargin aikata kisa ya bukaci alkalin da ke sauraron shari’ar ya daura aurensa da masoyiyarsa, ana tsaka da zaman kotu.

Ana dai tuhumar Kashwan Flower da harbe wani mutum a yankin York na Jihar Pennsylvania da ke kasar Amurka.

Lauyan wanda ake tuhumar, Attoni Brian Perry, ne ya gabatar da bukatar a gaban alkalin kotun a ranar Talata, ana tsaka da zaman kotu, yana mai roka masa alfarma alkalin ya daura aurensa da sahibarsa a kotun bisa la’akari da cewa masoyiyar tasa ba ta cikin wadanda za su bayar da shaida a shari’ar.

Lauyan, bayan mika bukatar wanda yake karewa, ya yi karin bayani cewa wannan ne karo na farko da ya taba neman irin wannan alfarma.

Duk da cewa alakalin kotun ya amince da bukatar, amma kuma ya bada sharadin cewa har sai an kammala shari’ar da ake yi.

Daga karshe kotu ta ci gaba da tsaron wanda ake tuhumar har zuwa gama shar’iar kuma ba tare da beli ba.

Ana zargin Kashwan Flower ne da harbe mutum da aka gurfanar da shi a kan zargin ya kashe a watan Agustan 2014.