✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Waliyyan Allah a ma’aunin Musulunci (1)

Godiya ta tabbata ga Allah Wanda da ni’imarsSa kyawawan ayyuka suke kammaluwa. Muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna neman tsarinSa daga…

Godiya ta tabbata ga Allah Wanda da ni’imarsSa kyawawan ayyuka suke kammaluwa. Muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah Ya shiryar babu mai iya batar da shi, wanda kuma Ya batar babu mai iya shiryar da shi. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba ya da abokin tarayya a gare Shi. Kuma na shaida Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma ManzonSa ne wanda Allah Ya aiko shi domin ya zama haske da shiriya gare mu baki daya.
Bayan haka, kuma Annabi mai tsira da amincin Allah ya fada a wani Hadisin kudusi cewa Allah Ta’ala Ya ce: “Duk wanda ya yi gaba da waliyyiNa hakika Na masa izini ya yi shirin yin yaki da Ni……….”
Yana daga cikin akidar Musulmi nagari wanda ya yi imani da Allah da ManzonSa ya gaskata tare da yin imani da samuwar waliyyan Allah da karamominsu. Lallai mumini na hakika yana imani da cewa Allah Yana da wadansu bayi nagartattu da Ya zabe su, Ya kuma dora su a kan aikin da’a gare Shi, Ya kuma daukaka su da soyayyarSa a gare su. Kuma yakan ba wasu daga cikinsu karamomi, Yana sonsu kuma Yana girmama su, kuma su ma masoyanSa ne suna yin soyayya da soyayyarsa, kuma suna fushi da fushinsa. Idan suka roke Shi sai Ya ba su, idan suka nemi taimakonSa sai Ya taimake su, kuma idan sun nemi tsarinSa sai yYa tsare su, kamar yadda Allah Ta’ala Ya ce: “Ku saurara! Lallai waliyyan Allah babu tsoro a gare su kuma ba za su yi bakin ciki ba. Su ne wadanda suka yi imani kuma suka kasance masu takawa.”
Duk da haka ya kamata Musulmi su sani cewa, waliyyan Allah ba  kamar yadda da yawa daga cikin masu raunin fahimta suke riyawa ba ne, ko kuma ma’abota bata suke nunawa, ko kuma kamar yadda ’yan bidi’a suke dauka cewa walliyyai wadansu kebantattun mutane ne a tsakaninsu kuma sanannu a gare su. Har ta kai suna kiran sunayensu, suna neman agajinsu suna neman taimakonsu suna riya cewa su ne masu cetonsu a wurin Allah ranar Alkiyama, har suna riya cewa suna saukar musu da arziki da alheri; suna saukar musu da talauci da bala’i yayin da suka yi fushi da su, suna neman warakar rashin lafiya daga gare su, alhali duk wadannan siffofi ne na Allah da kuma ayyukansa da babu wani mai hakki a ciki daga abin halitta, har Annabawa ba su da wannan iko.
Do haka a Musulunci waliyyan Allah su ne masu imani da Allah da kiyaye dokokinsSa, kuma su ne masu albishir da karama a nan duniya da Lahira, kuma hakika kowane mumini takiyyi, waliyyin Allah ne, kamar yadda Allah Ya fada: “Ku saurara! Lallai waliyyan Allah babu tsoro tare da su kuma ba za su yi bakin ciki ba. Su ne wadanda suka yi imani suka zamanto masu tsare dokokin Allah (takawa). Suna da albishir a rayuwar duniya da kuma Lahira, babu musanyawa ga kalmomin Allah wancan shi ne rabo mai girma.”
Sannan Allah Ya sake cewa: “Su ba su zamo waliyyanSa ba, abin sani waliyyan Allah su ne masu kiyaye dokokin Allah.” Daga wannan ayar ne malamai suka ce duk mumini mai tsare dokokin Allah, waliyyin Allah ne.
Sai dai abin sani game da waliyyai shi ne suna da matsayi mabambanta, gwargwadon imaninsu da tsare dokokin Allah. Duk wanda ya kasance rabonsa na imani da takawarsa ya fi cika, to darajarsa da daukakarsa (karamarsa) a wurin Allah sun fi. Saboda haka shugabannin waliyyai su ne Manzanni da Annabawa (SA) da wadanda suka biyo bayansu daga muminai a sahabbai da mabiyansu (tabi’ai) kamar yadda Annabi (SAW) ya fada daga Ubangijinsa dangane da waliyyai da karamarsu cewa: “BawaNa ba ya samun kusanci da Ni da abin da Na fi so a gare shi irin abin da Na wajabta masa, kuma bawaNa ba zai kusanta da Ni da nafilfili ba, face sai na so shi. Idan Na so shi zan zama jinsa da yake ji da shi da ganinsa da yake gani da shi da hannunsa da yake damka da shi da kafarsa da yake tafiya da ita. Kuma idan ya roke Ni zan ba shi bukatarsa, kuma idan ya nemi tsariNa zan tsare shi.”
Kuma Annabi (SAW) ya ce “Allah Yana da wadansu mazaje, da za su yi rantsuwa ga Allah sai Ya kubutar da su.” Abin da wannan Hadisi yake nunawa a nan shi ne; idan waliyyin Allah na gaskiya ya yi rantsuwa game da faruwar wani abu, to sai Allah Ya farar da wannan abu domin ya kubutar da rantsuwarsa.
Ya ku ’yan uwana a cikin imani! Ku sani abin da yake faruwa ko gudana ga mutane da ya saba wa al’ada ya kasu gida uku ne, akwai Mu’ujiza, akwai Karama, sannan akwai Istidraji. bari mu dauke su daya bayan daya domin mu san bambancin da ke tsakaninsu.
1. Mu’ujiza: Ita Mu’ujiza ba ta bukatar dogon bayani domin kowa ya san cewa tana kasancewa ne ga Annabawa da Manzanni (AS) idan aka kalubalance su. Misalin Mu’ujiza tana da yawa a cikin Littafin Allah kamar: Sandar Annabi Musa (AS) da taguwar Annabi Salihu (AS) da kuma Mu’ujizar Annabi Isah (AS) ta tayar da matattu da warkar da makafi da kutare da Babbar Mu’ujiza wato Alkur’ani Mai girma na Annabi (SAW) da sauransu.
Ibrahim IBB Kazaure,
[email protected]
07031616267.