✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wakilin AIT da iyalansa sun mutu a hadarin mota

Wakilin gidan talabijin na AIT, Mista Abdullahi Ibrahim da matarsa da ’ya’yansa uku sun mutu a sakamakon mummunan hadarin mota. Abdullahi, babban dan jarida ya…

Wakilin gidan talabijin na AIT, Mista Abdullahi Ibrahim da matarsa da ’ya’yansa uku sun mutu a sakamakon mummunan hadarin mota.
Abdullahi, babban dan jarida ya gamu da ajalinsa ne a hadarin motar da ya auku a tsakanin kauyen Ojodu da Ochadamu a kan hanyar Ajakuta zuwa Ayingba a kan hanyarsa ta zuwa kauyensu na Okaba da ke cikin karamar hukumar Ankpa da ke jihar Kogi don shirye-shiryen auren ’yarsa da za a yi a watan Disemba mai zuwa.
Rahotanni sun nuna yana tafiya ne a motarsa kirar kamfanin fujo 504 tare da ’ya’yansa uku da matarsa da ke dauke da juna biyu yayin da suka yi hadarin.