✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wakilan APC da PDP na samun miliyoyin Naira daga masu son tsayawa takara

Osinbajo ya bukaci bayanan asusun wakilai a Kano.

A yayin da masu son tsayawa takarar Shugaban Kasa a jam’iyyun APC mai mulki da PDP ke zawarcin kuri’u kafin zaben fid-da-gwani, wakilan jam’iyya wato daliget kasuwarsu ta bude, inda suke samun miliyoyin Naira, kamar yadda binciken Aminiya ya gano.

Mutum 38 ne ke fafata neman tikitin takarar Shugaban Kasa a manyan jam’iyyun biyu. Yayin da APC ke da 23, PDP ta rage yawan masu neman tikitin zuwa 15.

Akwai jimillar daliget 7,800 daga sassan kasar nan da za su yi wa manema takara na jam’iyyar APC alkalanci a zaben fid da gwani.

Su kuwa masu neman takara a PDP su 15, daligeti 3,700 ne za su kada musu kuri’a a ranar 28 da 29 don zaben daya daga cikinsu a matsayin wanda zai rike tutar jam’iyyar.

Kafin wannan rana masu neman takarar Shugaban Kasa suna tuntubar wakilai a jihohi, inda suke gwangwaje su da kyaututtuka daban-daban musamman kudi, don ganin sun samu amincewarsu.

Rahotanni daga jihohi sun nuna cewa daliget na samun abin duniya daga masu neman takara. Wani wakili ya shaida wa Aminiya cewa lokaci ne da kakarsu ke ci, kuma suna samun kudi.

A makon jiya jaridar Daily Trust ta yi rahoto na musamman kan yadda Dala ta yi tashin gwauron zabo, bayan da masu neman tsayawa takara ke kara bukatar ta kafin zaben fid-dagwanin.

Manyan ’yan takarar da suka karade fadin kasar nan domin neman goyon bayan daliget a Jam’iyyar APC sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Rotimi Amaechi da Kayode Fayemi.

A Jam’iyyar PDP kuwa wadanda suka gana da daliget daga wannan jiha zuwa waccan sun hada da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, da Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed da Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel. Sai tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi da hamshakin dan kasuwa, Mohammed Hayatu -Deen.

Osinbajo ya bukaci bayanan asusun wakilai a Kano

A ranar Talatar ce Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci Jihar Kano domin ganawa da wakilan Jam’iyyar APC.

Taron ya gudana ne a dakin taro na Coronation da ke Gidan Gwamnati inda aka hana ’yan jarida shiga.

Wani jami’in tsaro ya shaida wa manema labarai cewa “Umarni ne daga sama.”

Sai dai Aminiya ta lura cewa bayan an tantance daliget, an ga wani jami’in ayarin Osinbajo yana karbar bayanan asusun ajiyar bankin wakilan, inda aka ji daya daga cikin wakilan yana cewa “Ba tsaba ba ne, an tura sun shiga asusun banki.”

An ce shi ma Wike da ya ziyarci Kano, ya bayar da sabuwar mota ga shugabannin jam’iyyar.

Shugaban PDP a Gombe ya samu mota, daliget sun dara da jin alamar shigar kudi asusun bankinsu.

A Jihar Gombe kuwa wadansu ’yan takarar Shugaban Kasa hudu ne daga Jam’iyyun APC da PDP suka ziyarci jihar inda suka tattauna da daliget.

A Jam’iyyar APC, Osinbajo da Tinubu da Fayemi sun ziyarci jihar, yayin da a Jam’iyyar PDP, Wike da Bala Mohammed da Tambuwal da Udom Emmanuel ne suka ga wakilan.

Wike shi ne ya fara ziyarar a watan Afrilu, inda ya gana da shugabannin jam’iyyar tare da rakiyar tsohon Gwamna Jihar Ibrahim Hassan Dankwambo.

Wani wakilin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce Wike ya sanar da bayar da sabuwar mota ga Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar.

Wani wakilin kuma ya ce kowane daga cikin masu neman takarar Shugaban Kasa ya bayar da wasu makudan kudi, wadanda aka raba wa wakilan.

An bayyana cewa, a lokacin da Mohammed da Tambuwal da Udom suka ziyarci jihar kowanensu ya bayar da kudi, wadanda aka raba daidai wa daida ga shugabannin jam’iyyar da wakilai.

Haka kuma, a Jam’iyyar APC, su ma ’yan takara uku ne suka ziyarci jihar da suka hada da Osinbajo da Tinubu da Fayemi, inda suka gwangwaje wakilan da makudan kudi.

Wani wakilin ya bayyana cewa kudaden da ake raba musu kyauta ne kawai kafin Babban Taron Kasa.

Tinubu ya ba wakilan Kaduna Naira miliyan 60, Amaechi kuma miliyan 20.

Da dama daga cikin masu neman takarar suna zawarcin Kaduna, haka ya sa suke bayar da kudi masu tsoka ga daliget da fatar za su kada musu kuri’arsu.

Wakilan Kaduna sun ce suna jin su tamkar sarakuna, domin masu neman tsayawa takarar shugabancin kasa na rawar jiki don ganin sun gana da su.

A Jam’iyyar APC, manyan ’yan takara biyu, Tinubu da Amaechi tuni suka gana da daliget din, inda suka ba su kudade masu yawa.

Yayin da Tinubu ya bayar da Naira miliyan 60, Amaechi kuma ya ba wa wakilan Naira miliyan 20.

Daga Jam’iyyar PDP, Wike da Bala Mohammed da Saraki da sauran ’yan takara sun kai ziyara.

Daliget sun ce babu wani abu da aka ba su kai-tsaye duk da cewa Wike ya bayar da tallafin Naira miliyan 200 ga ’yan gudun hijira a Kaduna.

Daliget sun dara a Benuwai

A Jihar Benuwai, wakilan Jam’iyyar APC da PDP masu zaben fid-da-gwani na cikin annashuwa da jin dadi ganin yadda asusun ajiyarsu na banki ya cika.

Aminiya ta jiyo wadansu wakilai daga jam’iyyun biyu na cewa kudaden da suke samu a halin yanzu daga masu neman takarar Shugaban Kasa da na Gwamna sun sa su, sun fita daga halin kuncin tattalin arziki su da iyalansu.

Daya daga cikin wakilan ya ce, “Za mu more kudaden da muka samu.” Duk da cewa a ranar Talata ne masu neman takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar APC suka fara zuwa jihar, inda Tinubu ya bude kofa, sai dai har zuwa yanzu ba a san ko nawa daliget din suka samu ba.

Sai dai an ce Osinbajo ya aike da ayarinsa makonnin baya, inda kowane daliget ya samu Naira 50,000. Ana sa ran Osinbajo zai ziyarci daliget din jihar a cikin makon nan.

A bangaren Jam’iyyar PDP kuwa, biyu daga cikin wakilan da suka zanta da wakilinmu sun tabbatar da cewa sun karbi Naira 250,000 ko sama da haka daga hannun masu neman takarar Shugaban Kasa da suka kai musu ziyara.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Bala Mohammed da Saraki da Wike da Mohammed Hayatudeen da Tambuwal da kuma Atiku duk sun ziyarci jihar.

Cin hanci babbar illa ne ga dimokuradiyya —Kungiyoyi

Da take tsokaci game da irin wannan hali, Daraktar Cibiyar Dimokuradiyya da Ci-gaba (CDD), Idayat Hassan, ta ce zaben Najeriya zabe ne na kudi don haka kudi ke bayyana tsarin dimokuradiyyar kasar nan.

A cewarta, sayen kuri’un daliget ya zama al’ada a zabbbuukan da suka gabata, sai dai ana ganin zaben 1993 shi ne mafi inganci a tarihin Najeriya.

“A shekarar 2015 mun ga yadda aka sayar da kuri’a a kan Dala 2000 zuwa Dala 3000 a lokacin zaben fid-da-gwani na Jam’iyyar APC a Legas, inda ’yan takara suka kashe kimanin Dala miliyan 16 zuwa 24.

“Zaben fid-da-gwani na PDP a zaben 2019 bai bambanta ba, inda aka rika sayar da kuri’a a kan Dala 2000 zuwa 10,000 a Fatakwal.

“Ba da ci- hancin ga daliget shi ne babban lamarin da ya fi daure kai a lokutan zabubbukan wanda haka ne ke hana a tsayar da wadanda suka cancanta.

“Zaben badi na iya zama mafi muni a zaben fid-da-gwani yayin da ake kashe makudan kudi wajen neman kuri’u.

“Akwai babban aiki a gaba wajen dakile rawar da kudi ke takawa a siyasa,” inji ta.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Inganta Harkar Zabe (PER), Mista Ezenwa Nwagwu, ya ce ya zama al’adar manyan jam’iyyun siyasa su “Sayi kuri’un daliget, inda suke ganin tamkar hakan ne zai ba su nasara.

“Abin da yake faruwa a yanzu tamkar maimai ne, domin babu wani taron jam’iyyun siyasa tun daga 1998 zuwa yau wanda ba a yi mu’amala da kudade ba, daliget da shugabannin jam’iyyar sun kasance tamkar ’yan kasuwa a irin wannan lokaci,” inji Nwagwu.

A nasa bangaren, Babban Daraktan Ciyar Kare Hakkin Dan Adam da Ci-gabansa (&+5′), Dokta Ibrahim Zikirullahi, ya ce yin amfani da kudade wajen jawo hankalin daliget abu ne da bai dace ba.

Shugaban Kungiyar Sa-ido Kan Harkokin Zabe (TMG) kuma Babban Darakta a Cibiyar Kare Hakkin Jama’a (CISLAC), Malam Auwal Musa Rafsanjani, ya ce shigowar kudi a siyasa yana da illa ga dimokuradiyya da kasa baki daya.

A cewarsa, hakan na nuni da cewa ’yan siyasa ne ke da tasiri a kan daliget.

(Rahoto daga Ismail Mudashir, Abbas Jimoh (Abuja), Clement A. Oloyede (Kano), Haruna G. Yaya (Gombe), Hope A. Emmanuel (Makurdi), Lami Sadik (Kaduna) & Magaji l. Hunkuyi (Jalingo)