Wakilan jam’iyyar APC a Jihar Kaduna sun jaddada goyon bayansu na mika mulkin Najeriya ga yankin Kudu.
Wakilan sun yi wannan jawabi ne a Kaduna, yayin daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa kuma Ministan Sufuri mai barin gado, Rotimi Amaechi, wadanda ya je jihar neman goyon bayansu.
- Yadda dubun wasu masu garkuwa da mutane ta cika a Kaduna
- Ganduje ya sasanta da Barau, ya bar masa takarar Sanatan Kano ta Arewa
Wakilan sun nanata matsayin Gwamna Nasir El-Rufai na goyon bayansu a mika mulkin domin tabbatar da gaskiya da adalci.
El-Rufai, wanda ya bayyana cewa ya kawar da matsin lamba na sayen fom din shugaban kasa, ya bayyana cewa yana ganin ya kamata mulki ya koma Kudu domin yin adalci da gaskiya.
Gwamnan ya ce ya dade yana bayyana matsayarsa kan batun mika mulki ga yankin Kudu.
Da yake mayar da martani kan jawabin Sanata Ali Ndume, Babban Daraktan Yakin Neman Zaben Amaechi, El-Rufai ya amince da kawancen da suka yi da kuma gudunmawar da Amaechi ya bayar wajen tabbatar da nasarar APC a 2015.
El-Rufai, ya ce wakilan jihar za su saurari duk masu neman tsayawa takarar shugaban kasa da ke neman goyon bayansu.