✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wakar Nasara ta Sarki Dawuda

(2 Sam 22.1-51) Ina kaunarKa kwarai, ya Ubangiji! Kai ne Mai kare ni. Ubangiji ne Mai cetona, Shi ne garkuwata mai karfi. Allahna, Shi ne…

(2 Sam 22.1-51)

Ina kaunarKa kwarai, ya Ubangiji! Kai ne Mai kare ni. Ubangiji ne Mai cetona, Shi ne garkuwata mai karfi. Allahna, Shi ne Yake kiyaye ni, Lafiya nake sa’ar da nake tare da Shi, Yana kiyaye ni kamar garkuwa, Yana kare ni, Ya ba ni lafiya. Na yi kira ga Ubangiji, Yakan cece ni daga magabtana, Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Mutuwa ta daure ni tam da igiyoyinta, hallaka ta auko mini a kai-a-kai. Mutuwa ta daure ni tam da igiyoyinta, Kabari kuma ya dana mini tarko. A shan wahalata na yi kira ga Ubangiji, na yi kira ga Allahna domin neman taimako. A HaikalinSa Ya ji muryata, kukana na neman taimako ya kai kunnenSa. Sai duniya ta raurawa ta girgiza, harsashin duwatsu suka jijjigu, suka girgiza Saboda Allah Ya fusata! Hayaki ya yi ta tukakowa daga hancinsa, harshen wuta da garwashi suna fitowa daga bakinsa. Ya bude sararin sama, ya sauko kasa, tare da girgije mai duhu a karkashin kafafunsa. Ya sauko ta bisa bayan kerubobi, yana tafe da sauri a kan fika-fikan iska. Ya rufe kansa da duhu, giza-gizai masu duhu cike da ruwa, suna kewaye da shi. Kankara da garwashin wuta suka sauko, Daga cikin walkiya da take gabansa, suka keto ta cikin giza-gizai masu duhu. Sa’an nan Ubangiji Ya yi tsawa daga sararin sama, aka ji muryar Madaukaki. Kankara da garwashin wuta suka sauko. Ya harba kibansa, Ya watsa magabtana da walkiya Ya kore su. Kashiyar teku ta bayyana, tussan duniya sun bayyana, sa’ar da Ka tsauta wa magabtana ya Ubangiji, sa’ar da kuma Ka yi musu tsawa da fushi. Ubangiji Ya mika hannunSa daga samaniya Ya dauke ni, Ya tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi. Ya cece ni daga magabtana masu karfi, daga kuma dukan masu kina, gama sun fi karfina! Sa’ar da nake shan wahala suka auka mini, amma Ubangiji Ya kiyaye ni. Ya fisshe ni daga cikin hadari, Ya cece ni, don yana jin dadina. Ubangiji yakan saka mini, saboda ni adali ne, Yakan sa mini albarka, don ni marar laifi ne. Na yi biyayya da umarnin Ubangiji, ban yi wa Ubangiji Allahna tawaye ba. Na kiyaye dukan dokokinSa, ban yi rashin biyayya da umarninsa ba. Ya sani ba ni da laifi, Domin na kiyaye kaina daga mugunta. Don haka Ya saka mini, domin ni adali ne, gama ya sani ni marar laifi ne. Kai, ya Ubangiji, Mai aminci ne ga masu aminci, Kai nagari ne, cikakke ga kamilai. Kai Mai tsarki ne ga wadanda suke tsarkaka, Amma kana gaba da mugaye. Kakan ceci masu tawali’u, amma kakan kaskantar da masu girman kai. Ubangiji Yakan ba ni haske, Allah Yakan kawar da duhuna. Yakan ba ni karfin da zan fada wa magabtana, Da ikon rinjayar kagararsu. Wannan Allah dai! AyyukanSa kamilallu ne kwarai, Maganarsa abar dogara ce! Kamar garkuwa yake, ga duk mai neman taimako a wurinSa. Ubangiji Shi kadai ne Allah, Allah ne kadai kariyamu. Shi ne Allahn da Yake karfafa ni, Yana kiyaye lafiyata a kan hanya. Yana sa in tabbata lafiya nake tafiya, kamar barewa. Yana kiyaye ni lafiya a kan duwatsu. Yakan horar da ni don yaki, domin in iya amfani da baka mafi karfi. Ya Ubangiji Ka kiyaye ni, Ka cece ni, in zama babban mutum saboda Kana lura da ni, IkonKa kuma ya kiyaye lafiyata. Ka tsare ni, ba a kama ni ba, ban kuwa taba faduwa ba. Na kori magabtana, har na kama su, ba zan tsaya ba, sai na yi nasara da su. Zan buge su har kasa, ba kuwa za su tashi ba, za su fadi karkashin kafafuna. Kakan ba ni karfin yin yaki, Kakan ba ni nasara a kan magabtana. Ka kori magabtana daga gare ni, zan hallaka wadanda suke kina. Suna kukan neman taimako, amma ba wanda zai iya cetonsu, za su yi kira ga Ubangiji, amma ba zai amsa ba. Zan murkushe su har su zama kura Wadda iska take kwashewa, Zan tattake su kamar cabi a titi. Ka cece ni daga mutane masu tawaye, Ka nada ni in yi mulkin sauran al’umma, Jama’ar da ban santa ba, ta zama abin mulkina. Za su yi biyayya sa’ar da suka ji ni, baki za su rusuna mini, za su karaya, su fita, suna rawar jiki daga kagararsu.

Ubangiji Mai rai ne! Yabo ya tabbata ga Mai kare ni! Allah ne, Mai cetona! A yi shelar girmansa! Yakan ba ni nasara a kan magabtana, Yakan sa jama’a a karkashina, Yakan cece ni daga makiyana. Ka ba ni nasara a kan magabtana, ya Ubangiji, Ka kiyaye ni daga mutane masu kama-karya, don haka zan yabe Ka a cikin al’ummai, Zan raira maKa yabo.

Kullum Allah Yakan ba sarkin da Ya nada babbar nasara. Yakan nuna madauwamiyar kauna ga wanda ya zaba, Wato Dawuda da zuriyarsa har abada.