✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wakar batanci: Wole Soyinka ya hana Davido neman afuwar Musulmi

Farfesa Soyinka ya ce babu dalilin da Davido zai nemi afuwar Musulmi, alhali ...

Fitaccen marubucin Najeriya, Farfesa Wole Soyinka, ya bukaci mawaki David Adeleke (Davido) da ya yi watsi da kiraye-kirayen Musulmi na neman afuwarsu kan wakar batancin addininsu da ya dora a shafinsa.

Wakar Logos Olori da Davido ya dora a shafinsa na Twitter ta yamutsa hazo, inda Musulmin suka yi ta caccakar sa kan abin da suka kira batanci ga Musulunci a cikin wakar.

Musulmi sun hasala ganin yadda a cikin wakar aka nuna mutane suna tikar rawa a kan darduma bayan idar da sallah a gaban masallaci, inda suka nemi mawakin ya gaggauta goge bidiyon wakar, ya kuma nemi afuwarsu.

Tuni dai ya goge wakar da ya fara dorawa a ranar Juma’a, sai dai bai ba da hakuri ba kan wakar, wadda shi ne furodusa kuma kamfaninsa ya dauki nauyi, amma wani mawaki mai tasowa, Taiwo Olamilekan, ne ya rera.

Farfesa Soyinka ya ce babu dalilin da Davido zai nemi afuwar Musulmi, alhali tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya furta kalaman cin zarafi da addinin Kirista, amma Kiristoci ba su taba neman ya ba su hakuri ba.

Punch ta ruwaito Wole Soyinka a cikin wata sanarwa da ya fitar, yana cewa, “Babu abin ba wa Musulmi hakuri, haka ma babu abin da El-Rufai zai bayar da hakuri game da maganganunsa na baya.

“Don haka kada a yi mamaki idan mun yi hannun riga da Shehu Sani a kan wannan batu saboda ya nemi Davido ya ba da hakuri, a madadin al’ummar Musulmi.”

A cewarsa, haka kuma Kiristoci ba su nemi kowa ya ba su hakuri ba, kan dalibar nan Debora Yakubu, wadda wasu dalibai suka kashe saboda batanci da ta yi wa Musulunci a Jihar Sakkwato.