✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ga watan Ramadan a Najeriya — Sarkin Musulmi 

Ranar Litinin za ta zama 1 ga watan Ramadan na shekarar 1445 daidai da 11 ga watan Maris, 2024.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ba da sanarwar ganin watan Ramadan a na shekarar 1445/2024.

Hakan dai na nufin za a fara azumin watan Ramadan ranar Litinin a Najeriya.

Sarkin Musulmin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ce, “Yau Lahadi, 29 ga watan Sha’aban, Hijira 1445, daidai da 10 ga watan Maris, 2024, an kawo karshen watan Sha’aban.

“Mun samu labarin ganin watan Ramadan daga shugabanni da kungiyoyin addinin musulunci a wurare da yawa a kasar nan, kuma kwamitocin ganin wata sun tantance sahihancin bayanan.

“Bisa ga haka, gobe Litinin, 11 ga watan Maris ta zama daya ga watan Ramadan,” a cewar Sarkin Musulmi.

Ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yawaita addu’a a watan Ramadan.

Ya kuma nemi masu kudi a cikin al’umma da su taimaki talakawa da gajiyayyu a lokacin ibadar azumin, musamman da abinci da sauran abubuwan bukata.