✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke uba zai yi tsafin kudi da dan autansa

Ya kawo dan autansa mai shekara tara Najeriya daga kauyensu da ke kasar Jamhuriyyar Benin da nufin yin tsafin kudi da shi.

Wani magidanci da ya nemi yin tsafin kudi da dan autansa mai shekara tara ya shiga hannu.

Magidancin mai ’ya’ya biyar ya tabbatar cewa ya kawo dan nasa Najeriya ne daga kauyensu da ke yankin Kwatano a kasar Jamhuriyyar Benin da nufin yin tsafin kudi da shi.

Ya shaida wa ’yan sanda cewa “na amince in yi tsafin kudi da dan autan nawa ne” saboda tsananin yunwa da talauci da suka yi masa katutu da iyalinsa.

Ya ce ya yanke shawarar yin hakan ne bayan wani dan kawunsa da ke zaune a Legas ya shaida masa cewa zai zama hamshakin mai kudi idan aka yi tsafin.

A kan haka ne aka hada su da su wani wanda ya yi alkawarin sama musu bokan da zai aiwatar musu da tsafin.

Ya sanar hakan ne ofishin Runduna ta 2 ta ’Yan Sanda da ke Legas baya an cafke shi tare da wasu mutum uku da suka hada baki da shi.

Da yake tabbatar da haka, Mataimakin Shugaban ’Yan Sanda mai kula da yankin, Mohammed Ali, ya ba da umarnin a zurfafa bincike domin kamo sauran masu hannu a cikin lamarin domin su fuskanci hukunci.

Ya ce a yayin bincike bayan gano shirin mutanen, sai jami’an rundunar suka tuntube su ta waya a matsayin bokaye, har daga karshe suka sa rana da wurin da za su hadu domin aiwatar da tsafin a yankin Sango na Jihar Ogun.

A nan ne ’yan sanda suka yi musu kofar rago suka cafke su, kuma dukkansu sun amsa laifin da ake zargin sun aikata.