Daraktan Cibiyar Bunqasa Ilimi da Wayar da kan Jama’a (AWEDI) da ke Jos, kuma xaya daga cikin malamai masu yi wa alhazai wa’azi a Najeriya da Saudiyya, Sheikh Muhammad Sulaiman, ya nemi Gwamnatin Tarayya ta binciko dalilin da suka sa gwamnatin Saudiyya ta dawo da alhazai mata na Najeriya a bana.