Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya aiko Annabi (SAW) da gaskiya bayyananiya, muna gode maSa muna neman taimakonSa. |
Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Tsira Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam da iyalansa da sahabbansa da dukan wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ya ’yan uwa Musulmi! Idan aka ce neman ilimi ana nufin neman ilimi addinin
Musulunci. Sai da ilimin addini ne ake bauta wa Allah har Ya karbi ibadar. Kuma ilimi shi ne guzurin da zai dora mutum a kan hanya mikakkiya har zuwa gidan Aljanna a gobe Kiyama!
Hakika Allah Madaukakin Sarki Yana raba baiwarSa ga wanda Ya so, haka ma fahimta take kamar yadda Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (SAW): “Duk wanda Allah Ya nufa da alheri to zai fahimtar da shi addini.”
Duk wanda ba ya fahimtar addini to ya dauka Allah ba Ya nufinsa da alheri kuma ba Ya sonsa. Kuma masu ilimi na da matukar daraja kuma suna da kima.
Allah Madaukakin Sarki Ya kwatanta masu ilimin duniya kawai da jahilai, koda kuwa mutum ya kai matsayin Farfesa a wani fanni na ilimi. Muddin mutum bai san komai ba na ilimin addinin Musulunci to Allah Ya kira shi da jahili. Saboda haka ya zama wajibi Musulmi ya tashi tsaye ya nemi ilimi addini! Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: “Mafi yawan mutane ba su da ilimi, sai dai suna da ilimin zahirin rayuwar duniya (book ko sana’a).”
Ya ’yan uwa Musulmi! Mu nemi ilimin da zai haskaka mana lahirarmu. Neman ilimi na taimakawa wajen gusar da wata duk shubha da Yahudu da Nasara ke kawowa. Mu nemi ilimin addini domin bauta wa Allah!
Ya ’yan uwa! Masu ilimi suna da wata babbar daraja kamar yadda Allah Ya fada, inda Yake cewa: “Shin masu ilimi suna daidaita da marasa ilimi?”
Amsa a nan ita ce “A’a!”
Haka Allah Ya ba su wani matsayi cewa su ne masu tsoron Allah kamar a inda Yake cewa: “Lallai masu tsoron Allah kawai su ne masu ilimi.”
Kun gani ya ’yan uwa Musulmi! Duk wadannan darajoji sun samu ne sanadiyar ilimi.
Ilimin da aka fi kauna da so, shi ne ilimin sanin Allah. Mu san wannan sani na gaske, saboda shi ne rukuni na farko na sharuddan Musulunci. Ilimi ko na mene ne ya kamata kafin ka san shi ka fara sanin ilimin tauhidi tukun.
Duk ilimin da kake da shi muddin ba ka da ilimi addini, to kai jahili ne!
Mu tashi tsaye wajen neman ilimin sanin Allah da hukunce-hukuncensa, haka ya sa Manzon Allah (SAW) ya umarce mu da cewa: “Neman ilimi wajibi ne a kan Musulmi namiji da Musulma mace (wato kowa da kowa).”
Ilimi hanya ce ta samun shiga Aljanna. Imam Tirmizi ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce “Duk wanda ya kama hanya ta neman ilimi, Allah zai sauwake masa hanya har zuwa cikin Aljanna.” Wannan duk daraja ce ta ilimin addini. Wani Hadisin da ke kara nuna mana muhimmancin neman ilimi yana cewa: “Duk wanda ya fita neman ilimi yana daidai da wanda ya fita jihadi.”
Ku dubi girma irin na jihadi amma an kwatanta neman ilimi da jihadi. Don haka wajibi ne kowane Musulmi ya nemi ilimin day a zama farilla a kansa kamar na ibadojin da suke kansa da kuma na sana’a ko kasuwanci ko aikin da yake yi. Idan har ba ya neman ilimi to ya tabe kuma ya yi asara. Abdullahi bn Mas’ud (RA) ya ce, ana neman ilimi ne ta wadannan hanyoyi: Kodai ka kasance malami mai ba da ilimi kuma yana nema, ko kuma ka kasance dalibi mai neman ilimi, ko ka kasance mai sauraren masu ilimi, (wato idan ya zamanto ba ka zuwa wajen neman ilimi to ya kamata ka zama mai saurare, kamar su huduba da wa’azi da wuraren bayar da ilimi da kuma samunsu a kafofin sadarwa na intanet da sauransu). Idan ba ka cikin wadannan, to tabbas za a lissafaka cikin jahilai!
Abu Darda’i ya ce “Ilimin da Allah Yake so shi ne ilimin addini.”
Hadisi daga Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Malamai su ne magada Annabawa, Annabawa kuwa ba su barin gadon zinari ko azurfa, sai dai sun bar gadon ilimi. Wanda duk ya yi riko da shi hakika ya yi riko da babban rabo.”
Ilimin zamani yana da kyau kuma yana amfani kuma yana muhimmanci, idan aka yi aiki da shi wajen taimako addini!
Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: “Allah Ya shaida babu wanda ya cancanci bauta sai Shi, Mala’iku sun shaida masu ilimi ma sun shaida.”
Allah Ya ba mu labarin Annabi Musa (AS), kan yadda duk da ilimi da baiwar da Allah Ya yi masa, amma da ya ji labarin wani mai ilimin (Annabi Khidir AS), sai da ya je wajensa neman karin ilimi.
Mai littafin Ta’alimi yana cewa: “Ana neman ilimi ne tun daga tsumman goyo har zuwa shiga kabari. Kun ga ke nan kowane lokaci cikin neman ilimi muke!
Idan akwai wanda ya fi kowa ilimi a wancan lokacin, to Annabi Musa (AS) ne, amma ga shi kuma bai yi girman kai ba wajen neman ilimi a wajen wanda ya ji ya fi shi ilimi.
Don haka malamai da dalibai kalubalenku, dole a tashi a kara neman ilimi, kada ka ce ai ni yanzu na gama karatu. Ku dubi matsayi irin na Manzon Allah (SAW), amma Allah Ya ce masa “Ka ce “Ya Ubangiji! Kara mini ilimi.’
Kuskure ne babba mai neman ilimin addini ya ce shi fa ya gama neman ilimi! Kada mutum ya zama daga ya sauke Alkur’ani ko ya iya Kawa’idi ya ce ya gama karatu!
Ilimi nemansa jihadi ne kamar yadda ayar nan ke fada wa sahabbai cewa: “Ya cancanta kada dukanku ku je jihadi, wadansu su tsaya karatu wadansu su je jihadi, (wadanda ke gida sai su koya wa wadanda suka je jihadi ilimin da suka koya).”
Allah Ya ba masu ilimi matsayi da dama. Allah (SWT) Ya fadi a cikin Alkur’ani cewa: “Ku tambayi ma’abota ilimi idan kun kasance ba ku sani ba.”Haka yana cewa: “Kada ka yi magana a kan abin da ba ka da sani a kansa. Ji da gani da tunanin dukansu ababen tambaya ne.”
Manzon Allah (SAW) ya ba ka dama ka yi ta kwadayin abu biyu. Wanda bai taba ba da irin wannan damar ba. Ya ce: “Babu wani kwadayi da za ka yi sai a abu biyu; ka yi kwadayin zama mai kudi na halal kana taimakon musulunci, kuma ka yi kwadayin zama mai ilimi da aiki da shi da koyar da shi.” Su kadai ne ake kwadayin samu!
Aliyu bn Abu Dalib (RA), ya ce ilimi abin nema ne, jahili ba ya so a ce masa jahili. Sai dai yana so a kira shi da mai ilimi duk da kuwa ba ya da shi!
Sarki yana hukunci ga talakawa shi kuwa sarki mai ilimi ne ke yi masa hukunci. Duk sarki mai hankali yana da malamin kirki mai ba shi fatawa.
Ya ku ’yan uwa Musulmi! Mu dunguma wajen neman ilimin addini, mu tabbatar da ’ya’yanmu da iyalanmu suna neman ilimin addini. Domin wajibi ne mu ba su ilimi, kamar yadda Allah Ya umarce mu cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kiyaye kawunanaku da na iyalanku daga wata wuta wadda makamashinta (abincinta) shi ne mutane da duwatsu. Akanta akwai matsara, Mala’iku masu karfi da tsanani. Ba su saba wa Allah a kan umarnin da Ya ba su, kuma suna aikata abin da aka umarce su da shi.”
Idan kana da ilimi to ka sanar da iyalanka, idan ba ka da lokaci, to ka dauki nauyin karatunsu na addini.
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Fiyayye a cikinku wanda ya koyi Al’kur’ani kuma ya koyar da shi.”
Sahabbai misali ne gare mu na irin gwgwarmayar da suka yi wajen neman ilimi, kama daga Abu Huraira da Abdullahi bn Umar da sauransu.
A’isha (RA), ta ce “Kur’ani rayuwa ce ta Annabi (SAW) saboda yadda yake yawan tilawarsa.”
Ya Allah! Ka ba mu ilimi mai amfani, kada Ka ba mu marar amfani! Ka karbi ibadunmu, Ka karbi salloli da addu’o’inmu! Ka yafe mana, Ka biya mana bukatunmu, amin.