Cikin wani tsohon hoton bidiyo da a cikin ‘yan kwanakin nan ya sake bayyana tare da karade zaurukan sada zumunta, an ji daya daga cikin ministocin Shugaba Muhammadu Buhari yana sukar gwamnati saboda kara farashin man fetur.
A dadadden bidiyon, an ji Ministan Sadarwa na yanzu, Dokta Isa Ali Pantami, yana Allah-wadai da tsohuwar gwamnatin Najeriya karkashin jam’iyyar PDP sakamakon tsawwala farashin man fetur da ta yi a baya.
A daya daga cikin mimbarinsa na wa’azi da tafsirin Al-kur’ani mai girma, Dokta Pantami tun gabanin ya shiga gwamnati, ya caccaki tsohuwar gwamnatin Najeriya ta PDP da cewa ba ta tausaya talakawan kasar.
Tun a wancan lokaci, Pantami ya yi tir da kara farashin man fetur a kasar, matakin da ya ce an dauka ne duk da ikirarin ga gwamnatin ke yi na cewa ana yi wa talaka sauki ta hanyar biyan kudin tallafin mai.
- Sojoji sun fatattaki ’yan bindiga a Nasarawa da Biniwai
- Yadda jarumar Bollywood Kangana ta sa zare da ’yan sanda
Shehin Malamin wanda ya fito daga jihar Gombe, ya kuma soki kudin da gwamnatin wancan lokaci ta yi da’awar ta na kashewa a matsayin tallafi domin rage tsadar man fetur a kasar.
Baya ga bayyana takaicinsa kan tsadar man fetur, Shaikh Pantami ya ce hukumomi da jami’ai su na bi su na karbar kudi a hannun ‘yan acaba da masu motar haya da ke neman na abinci.
Ga abin da Shaikh Pantami ya ke fada a bidiyo na fiye da tsawon rabin minti: “Saboda su a tunaninsu, sun ma dauka wannan wutar kamar hasken rana ne da ba a dauke ta.”
“Amma N2.7tiriliyan, wai a haka subsidy ne, wai kudin rarar mai, kuma an zo an kara kudin mai, talaka ya kara shiga cikin kunci na rayuwa, rayuwa ta kuntata kuma a haka ake tatsar ‘dan acaba, mai opel an tatse shi, a kullum za a ci N200, N300.”
“A haka a tara biliyoyi, kuma wani ya je ya hau kansu ya kwanta.”