✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Waiwaye: Yadda Rufe Hanyoyin Sadarwa Ya Shafi Harkokin Kasuwanci

Domin sauke shirin latsa nan Wayar tarho da intanet sun kama hanyar zama jinin jikin al’umma a wannan karni na 21. Alakar mutane da hanyoyin…

More Podcasts

Domin sauke shirin latsa nan

Wayar tarho da intanet sun kama hanyar zama jinin jikin al’umma a wannan karni na 21.

Alakar mutane da hanyoyin sadarwa ta zamani ta sa kusan harkokin kasuwanci sun tasamma komawa intanet, a wasu lokutan kuma ana amfani da wayar tarho ne wurin assasa harkokin kasuwanci da kuma tabbatar da su.

Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi waiwaye kan irin halin ni-’yasun da harkokin kasuwancin suka shiga a sakamakon rufe layukan sadarwa a kwanakin baya a Jihar Katsina.