A wannan mako ne aka buga wasa na biyar na kakar bana ta gasar Firimiya ta Najeriya (NPFL), inda wasu kungiyoyi suka buga wasansu na farko.
A wasannin da aka buga, an kece-raini a tsakanin kulob din Niger Tornadoes da Enugu Rangers, inda Enugu Rangers ta lallasa Niger Tornadoes da ci daya da nema. Haka kuma kulob din na Niger Tornodoes ya sha kashi da daya nema a wasa na uku a hannun Wikki Tourist na Bauchi.
A minti na 33 ne dan wasan Enugu Rangers mai suna Silas ya jefa kwallo a ragar Niger Tornadoes, sannan aka ci gaba da taka leda har aka tashi.
A Damaturu kuma, kulob din Yobe Desert Stars ne ya lallasa takwaransa na Gombe United da ci daya da nema, bayan Usman Abdullahi ya jefa kwallon daya mai ban haushi a ragar Gombe.
Haka ma kulob din Wikki Tourist ya lallasa kulob din Bendel Insurance da ci daya da nema a filin wasan Pantami da ke Jihar Gombe.
Sulaiman Muhammed ya jefa kwallon a ragar Insurance bayan masu tsaron gidan sun takfa kuskure, inda shi kuma bai wata-wata ba, ya zura kwallon ya bar su da tagumi.
Jibi, Lahadi 3 ga Fabrairu ce za a ci gaba da kece-raini a wasa na 6 na gasar.