A ranar Juma’ar da ta gabata ce Crystal Palace da Arsenal suka bude taro da wasan makon farko na gasar Firimiyar Ingila ta bana da ta kankama gadan-gadan.
Arsenal wadda ta taba lashe gasar sau 13 a tarihi, ta yi nasara a wasanta na farko inda ta lallasa Crystal Palace da ci biyu da nema.
- ’Yan bindiga sun sace amarya da angonta a Katsina
- Gwamnoni sun shawarci Buhari ya kori ma’aikatan da suka haura shekaru 50
Wasa na biyu da aka buga a wasannin makon farko na gasar shi ne wanda Fulham ta karbi bakuncin Liverpool a Craven Cottage da aka tashi canjaras 2-2.
Bournemouth ta yi kokarin kare mutuncin gidanta yayin da ta lallasa Aston Villa a wasansu na ranar Asabar da aka tashi 2-0.
Nottingham Forest ta yi rashin nasara a bakuntar da ta kai wa Newcastle United a St. James Park, inda aka tashi wasan biyu babu ko daya.
Rubdugun kwallaye 4-1 gami da babu sani babu sabo Tottenham United ta nuna wa Southampton a haduwar da suka yi ranar Asabar, lamarin da ya sa kungiyar ta Arewacin Landan ta yi dere-dere a saman teburin Firimiyar Ingila da maki uku, inda ta yi wa kowacce kungiya fintikau da yawan kwallaye.
Wolves ta kwashi kashinta a hannu yayin da ta je bakunta gidan Leeds United wadda ta zuba mata kwallaye 2-1 a filin wasa na Ellan Road.
Ana iya cewa da kyar Chelsea ta samu maki uku da ci daya mai ban haushi a wasanta da Everton yayin ziyarar da ta je Goodison Park.
Karfi ne ya zo daya a wasan da aka tashi 2-2 tsakanin kungiyar Leicester City da Brentford a filin wasa na King Power.
Lamarin Manchester United dai kusan jiya-i-yau, domin kuwa ba ta wani sauya zani ba kamar yadda ta kasance a kakar wasannin da ta shude.
United dai ta sha kashi a hannun Brighton da ci 2-1 a Old Trafford a wasan farko da ta fara na Firimiyar Ingila ta bana.
Brighton ce ta fara cin kwallo ta hannun Pascal Gross saura minti 15 a tafi hutun rabin lokaci, sannan shi ne ya kara ta biyu da tazarar minti tara tsakani.
Pascal Gross ya ci Manchester United kwallo shida a Firimiyar Ingila shi kadai – shi ne kan gaba dan wasan Brighton da ya ci United kwallaye da yawa a gasar.
United ta zare daya bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci, bayan da Alexis Mac Allister ya ci gida, saura minti 22 a tashi daga wasan.
Wannan dai shi ne karon farko da kungiyoyin suka buga wasan bude Firimiyar wato makon farko a tsakaninsu.
A kakar da ta wuce, Brighton ta doke United 4-0 ranar 7 ga watan Mayu, bayan da tun farko United ta ci Brighton 2-0 a ranar 15 ga watan Fabrairun 2021.
Ita kuwa Manchester City mai rike da kambun Firimiyar Ingila, ta fara kakar bana da kafar dama, bayan da ta je ta doke West Ham United da ci 2-0 ranar Lahadi.
Sabon dan wasan da City ta dauko a bana, Erling Haaland, shi ne ya ci mata kwallon farko a bugun fenareti, kuma shi ne dai ya kara ta biyu a raga.