Wahalar takardun kudaden Naira 200, 500 da 1,000 ta fara dawowa a Jihohin Kano da Borno yayin da wa’adin daina amfani da su na ranar 31 ga watan Disamba ke dada karatowa.
A watan Maris din da ya gabata ne dai Babban Bakin Najeriya (CBN) ya sanar da cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudaden har nan da karshen shekara kamar yadda Kotun Koli ta bayar da umarni.
- Gwamnati ta raba wa mata masu karamin karfi 15 injin niƙa a Edo
- Ta mutu tana saduwa da saurayinta da ya sha maganin karfin maza
Tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ne ya sanar da canjin kudin a watan Oktoban bara, lamarin da ya tsayar da komai cak a kasar.
Hakan ya kuma haifar da zanga-zanga a sassan Najeriya daban-daban, wasu wuraren ma har da farfasa bankuna.
To sai dai yayin da ya rage wata biyu kafin cikar wa’adin, Aminiya ta gano cewa yanzu ’yan kasuwa sun fara kokawa da dawowar wahalar kudaden.
Sai dai wani jami’in Babban Bankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar mana da cewa sam ba su da shirin janye tsofaffin kudaden gaba daya.
Shi kuwa wani mai sana’ar POS a Kano, Abdullahi Usman, ya ce a yanzu abin da bankuna ke barin daidaikun mutane su cire a kullum ba ya wuce Naira 40,000 zuwa 50,000, yayin da kamfanoni ba ya wuce 150,000 zuwa 200,000.
Abdullahi ya ce yakan samu kudaden shi ne daga kasuwannin da ake hada-hadar kudade, ba daga bankuna ba.
“Idan ka shiga gari yanzu, za ka ga akasarin masu POS ba su da kudade kamar yadda suke da su a makonnin baya,” in ji shi.
Ya ce karatowar wa’adin na CBN ya sa yawancin mutane yanzu sun shigar da kudadensu bankuna saboda gudun samun matsala.
Shi ma wani mai sana’ar ta POS mai suna Bello Shehu, ya ce yanzu da gidajen mai ga dogara domin samun takardun kudade saboda bankuna ba su da su.
“Yanzu galibi da gidajen mai muka dogara, saboda kudaden da muke samu daga bankuna ba za su ishe mu biyan bukatun abokan huldarmu ba,” in ji Bello.
Kodayake babu dogayen layuka a na’urorin cirar kudi na ATM, amma Aminiya ta lura akasarinsu babu kudi a ciki.
Shi ma wani mai shago a unguwar Hotoro da ke Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano, Muhammad Gambo, ya ce ya ɗan kwana biyu ba ya samun kudade daga ATM.
Shi ma wani ma’aikaci da ke aiki da Gwamnatin Jihar Kano ya ce sai da ya ce ATM shida domin cire albashinsa na watan Oktoba, amma babu kudi a ciki. Ya ce daga karshe sai a wajen masu POS ya iya samun rabin abin da yake nema.
Daga Hamisu K. Matazu (Maiduguri), Abiodun Alade (Legas), Philip S. Clement (Abuja) da Sani Ibrahim Paki