Kungiyar Dillalan Man Fetur mai zaman kanta ta Kasa, IPMAN ta yi gargadin cewa ’yan Najeriya za su fuskanci wahalar man fetur da ba a taba ganin irin ta ba a tarihin kasar.
IPMAN ta ce za a fuskanci matsanancin karancin man fetur a gidajen mai muddin Hukumar NMDPRA mai sa ido kan harkokin man fetur ba ta biya su kudaden dakon mai ba.
- Gwamnonin Arewa da suka saya wa Jonathan fom din takara
- 2023: Ba mu muka saya wa Jonathan fom din takara a APC ba — Miyetti-Allah
Shugaban IPMAN shiyyar Kano, Bashir Ahmad Danmalam ne ya yi wannan gargadi a wani taron manema labarai a Kano a ranar Litinin.
Danmalam ya ce wahalar man fetur din da ’yan Najeriya a yanzu suka fara fuskanta musamman a Abuja, babban birnin kasar somin tabi ce.
A cewarsa, rashin biyan kudin dakon, wanda adadin sa ya haura Naira biliyan 500, ya sanya da yawa da ga cikin dillalan sun durkushe, yana mai cewa daga cikin kaso 100 na dillalan man, biyar ne kawai suke iya dakonsa a yanzu.
Ya kara da cewa rashin biyan kudaden da NMDPRA ta yi ya sanya wasu ’yan kungiyar sun kasa ma dakon man zuwa jihohin kasar nan.
Sai dai Danmalam ya ce akwai wadataccen mai a daffo-daffo a kasar nan, amma ’yan kungiyar ba za su ci gaba da dakon shi zuwa jihohi ba saboda kin biyansu makudan kudaden da ba a yi ba kuma hakan a cewarsa, ya yi wa kasuwancinsu illa.
“Wasu fa bashi ma su ka ci na banki su ke harkar nan. Wadannan kudaden da mu muke tara su domin a samu daidaito wajen farashin man fetur yadda ’yan kasa za su samu sauki.
“Mu na da wadataccen mai a kasa, amma ba za mu iya ci gaba da rarrabawa ba sabo da an ki biyanmu kudadenmu na dako.
“In dai ba a biya mu kudaden nan ba, to ’yan kasa su shirya ganin wahalar man fetur da ba a taba ganin irin ta ba,” in ji Danmalam.
Ya kara da cewa tun sanda a ka kafa Hukomin da ke kula da harkokin man fetur na PEF, DPR, da PPRA suka rikide suka zama NMDPRA a bara, sau biyu ta taba biyansu kudaden, inda ya koka cewa yanzu su na bin kudaden na wajen watanni 9.
Bayan ya yaba wa kamfanin mai na NNPC bisa kokarin tara wadataccen man fetur, Danmalam ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sanya NMDPRA ta biya su kudaden su domin kawo karshen matsalar a kasa baki daya.
Hutun Sallah ne ya janyo wahalar man fetur —NNPC
Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya alakanta wahalar man fetur din da ta sake kunno kai a wasu sassan Najeriya da karancin dakon shi saboda hutun Sallah.
Gidajen mai da dama dai a Abuja da Kano da Legas sun kasance a rufe.
A cewar Shugaban Sashen Yada Labarai na kamfanin, Garbadeen Muhammad cikin wata sanarwa, NNPC ya ce, “Kamfanin NNPC ya lura da sake dawowar dogayen layukan mai a wasu sassa na Abuja.
“Hakan ba abin mamaki ba ne in aka yi la’akari da karancin dakon man sakamakon dogon hutun da ake tafiya, kamar hutun Sallah Karama a wannan karon.
“Wani abin kuma da ya dada ta’azzara matsalar shi ne karin bukatar man, wacce ke faruwa a duk lokacin da mazauna Abuja suke dawowa daga hutu,” inji sanarwar.
Sai dai NNPC ya ce ya dauki matakan ganin cewa ya yi aiki da hukumomin da ke kula da rarraba shi don ganin ya wadata a ko ina.
“Muna ba dukkan mazauna Abuja da ma dukkan ’yan Najeriya tabbacin cewa muna da wadataccen mai a ajiye, wanda yawan shi ya haura lita biliyan biyu da rabi, kuma zai iya yin kwana 43,” inji kamfanin.