Gwamnatin Tarayya ta gargadi ’yan kasuwa da su daina boye man fetur da gangan wanda hakan ya jefa wasu jihohin kasar nan cikin mawuyacin hali.
Wata sanarwa da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA), ta fitar ta ce babu wani shiri na kara farashin man fetur a nan kusa.
“Gwamnati na sanar da jama’a cewa ba ta da niyyar kara farashin man fetur a wannan lokacin.
“Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) na ci gaba da shigo da mai cikin kasar kuma wanda ke kasa zai isa har tsawon kwanaki 34.
“Saboda haka, ana shawartar ’yan kasuwa su guji boye man, jama’a kuma su daina fargaba.
“Duk ’yan kasuwar da aka gano suna boye man fetur za a sanya musu takunkumi,” in ji sanarwar hukumar..
Ta jaddada cewa za ta ci gaba da sanya ido kan yadda ake samarwa da kuma rarraba man fetur a fadin Najeriya musamman a wannan lokacin da bukukuwa ke karatowa.
Masu ababen hawa musamman a Jihar Legas da Abuja na shan wahala wajen samun man fetur a gidajen mai.
Karancin man ya janyo dogayen layukan a gidajen mai a yayin da masu ababen hawa da ’yan kasuwa ke yunkurin sayen mai, wasu kuma ke saya a hannun ’yan bunburutu.
Lamarin ya kawo cunkoson ababen hawa a wasu manyan tituna saboda yadda masu ababen hawa ke tare titunan shiga manyan garuruwa.
A halin da ake ciki, Kungiyar Dillancin Man Fetur ta Najeriya (IPMAN), ta ce mambobinta na samun litar man fetur a kan sama da Naira 200.
Hakan ya sanya a wasu jihohi kamar Legas, Kano, Kaduna da kuma Abuja, masu ababen hawa ke shan man a N250 zuwa N265 kan kowace lita.