Gwamnatin Sri Lanka ta amince da karin kwanakin hutun karshen mako zuwa kwana uku har zuwa tsawon wata uku masu zuwa ga galibin ma’aikata, sakamakon matsalar karancin man fetur din da kasar ke fuskanta.
Wani babban Ministan kasar ya ce ranar Juma’a za ta kasance ranar hutu ga yawancin ma’aikatan da ke aiki a ma’aikatun da ba na bukatu ta musamman ba.
- Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya mutu bayan ya taka nakiya a Mali
- Shugaban Amurka ya auna arziki bayan faduwa a keke
Tsarin ba zai shafi ma’aikata a muhimman sassa kamar bangaren kiwon lafiya da makamashi da ilimi da kuma tsaro ba.
Sri Lanka ta shiga fatara a asusun ajiyar kudadenta na waje kuma karancin shigo da mai ya haifar da wahalar mai a cikin kasar.