Hukumar Shirya Jarabawa ta Yammacin Afirkta (WAEC) ta dage ranar fitar da sakamakon jarabawarta na kammala sakandare da aka gudanar bana zuwa mako mai zuwa.
A ranar Laraba 28 ga Oktoboa ya kamata WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar amma ta ce ta dage saboda rikici da kone-konen da aka yi a boren #EndSARS a sassan Najeriya.
“A yau Hukumar ta shirya fitar da sakamakon jarabawar amma dokar hana fita da aka sanya a makon jiya ya sa aka dage fitar da sakamakon zuwa makon gobe. Nan gaba za a sanar da ainihin ranar”, inji sanarwar da WAEC ta wallafa a shafinta na Twitter.
Jami’in Hulda ja Jama’a na Ofishin Hukumar a Najeriya, Demianus Ojijeogu, ya tabbatar da hakan.
Idan ba a manta ba bullar annobar COVID-19 da dokar kulle da aka sanya domin dakile yaduwarta ta sanya an daga gudanar da jarabawar a Najeriya da wasu kasashe.
A baya an saba gudanar da jarabawar ne tsakanin watan Mayu da Yuni, amma bullar a annobar ta sa a 2020 aka gudanar a watan Agusta.