Hukumar Shirya Jarrabawar ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta sanar da ranar Litinin, 16 ga watan Agustan 2021 a matsayin ranar da za a fara rubuta jarrabawar kammala sakandire (WASSCE).
Babban jami’in hukumar a Najeriya, Mista Patrick Areghan ne ya sanar da haka a Legas ranar Talata.
- Kwalara ta kashe mutum 4, ta kama 48 a Gombe
- An kashe mutum 112, an sace 160 a Kaduna da Filato a wata daya – Rahoto
A cewar sanarwar, “La’akari da jadawalin da aka amince da shi na kasa da kasa, jarrabawar WASCCE ta shekarar 2021 a dukkan yankin da ake rubutata za ta gudana daga ranar Litinin 16 ga watan Agusta zuwa Juma’a, takwas ga watan Oktoban 2021.
“To sai dai a Najeriya, za a kammala jarrabawar ne ranar 30 ga watan Satumban 2021, bayan an shafe makonni bakwai kenan ana yinta,” inji sanarwar.
A baya dai, akan rubuta jarrabawar ne a tsakanin watannin Afrilu da Mayun kowacce shekara, in ban da a bana da aka sami tsaiko sakamakon yadda annobar COVID-19 ta kawo dagula lamura.