Kwamishinonin ilimi a Arewacin Najeriya sun goyi bayan Gwamnatin Tarayya kan dage bude makarantu ga dalibai masu kammala firamare da kuma karama da babbar sakandare.
Jihohin masu makarantun musayar dalibai sun ce Ministan Ilimi Adamu Adamu ya yi daidai da ya ce domin kare rayuka, ba za a bude makarantun ba, ko da kuwa Najeriya za ta yi asarar jarabawar kammala sakandare ta WAEC na shekarar 2020.
“Mun yi ittifaki cewa ba za a bude makarantu ba sai an tabbatar da kariyar rayuka, sannan dukkan jihohi sun bi mafi karancin ka’idojin kariyar COVID-19 yadda NCDC ta gindaya”, inji su.
Sun kuma ce dole “kowace jiha ta yi cikakken nazarin halin da makarantunta ke ciki sannan ta mika wa gwamnanta rahoto da ke tabbatar da cewa kowace makaranta na da dukkanin kayan kariya da NCDC ta ayyana, domin yanke hukunci”.
Sanarwar dauke da sa hannun shugabansu kuma Kwamishinan Ilimin Jihar Kaduna, Shehu Usman Muhammad ta ce dalibai za su shiga jarabawar WAEC ko wata jarabawa ce idan da tabbacin tsaron lafiyarsu bisa kulawar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.
Sun kuma bukaci Gwamnatin Tarayya ta taimaki jihohi da tallafin COVID-19 domin samar da muhimman kayayyakin kariya a makarantu, kasancewar yawancinsu ba su da karfin tattalin arziki.
Yin hakan a cewarsu zai yiwu da kudaden tallafi da gwamnatin ta samu daga hukumomin agaji na duniya.
Taron ya samu halarcin Kwamishinonin ilimi 13 daga jihohin Kaduna, Bauchi, Gombe, Niger, Nasarawa, Adamawa da Taraba.
Sauran su ne na Kogi, Kwara, Katsina, Kano, Borno da kuma jihar Jigawa.