Rundunar ‘Yan sandan Jihar Borno ta samu nasarar kama wadanda ake zargi da cin zarafin wata budurwa mai suna Fadila Abubakar bisa zarginta da kushe dan majalisa a Facebook.
Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, CP Abdu Umar ne ya sanar da hakan a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da yake yi wa manema labarai bayani game da lamarin.
- Kisan Hanifa: Dalilin da aminci zai kau tsakanin iyayen dalibai da malamai
- Fasa Janye Tallafin Mai: Gwamnoni Sun Goyi Bayan Kungiyar Kwadago
A cewarsa, Sufeto Janar na ‘yan sanda Usman Alkali Baba da Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum sun kadu matuka da lamarin cin zarafin budurwar, wanda ya karade kafafen sadarwa, inda ya ce lamari ne na yaudara da cin zarafin da duka da mallakar muggan mukamai da kuma sata.
CP Umar ya ce, “a ranar 23 na wannan watan da misalin karfe 14:30, an zargi wasu ‘yan daba magoya bayan Honorabul Injiniya Satomi Ahmed, Dan majlisa mai wakiltar Jere a Majalisar Wakilai da daukar wani mai suna Sa’adu Suleiman da ake wa lakabi da Manu Nakande, inda suka kai farmaki gidan abincin Zahura Restaurant da ke dandalin shakatawa na Maiduguri, kuma suka kai hari ga Fadila Ibrahim mai shekara 29 da wani mamba na kwamitin hulda da jama’a na ‘yan sanda, waddaa suka buge ta sannan suka tarwatsa gidan abincinta, sannan suka tafi da wayarta.
“Kawai saboda suna zarginta da yada wani hoto da rubutu da suke zargin ta bata sunan ogansu.”
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce wannan ya sa suka shiga aiki, inda suka samu nasarar kama wadanda ake zargi.
Wadanda aka kama su ne: Nasiru Abubakar mai suna Mana da Bello Mudassir mai suna Alshabab da Ali Dungus Shettima mai suna Ari da Malan Mohammed mai suna Bonboy.
Daya daga cikin wadanda ake zargi da kai wa Fadila farmaki, Nasiru Abubakar mai shekara 22 ya ce wani mai suna Manu Nakande ne ya tura su. “Ni ne na tambaye ta me ya sa ta yi wannan rubutun a Facebook.
“Na ce mata me ya sa ta yi wannan zunubin? Sai ta ce Injiniya Satomi ya yi mata alkawarin wani abu amma bai cika mata alkawari ba.
“Sai na ce da bai cika mata alkawarin ba me ya sa ba ta same shi a gida ba?
“Ba na nan lokacin da aka kai hari a gidan abincinta domin bai ce mu tarwatsa mata gidan abinci ba, amma tunda hakan ya faru, dole a zarge mu.
“Kawai ya ce mana ne mu tozarta ta. Ni ne na mare ta a wannan bidiyon. Na mari Fadila sau hudu ko sau biyar.”
“Da gaske an ba ni 7000, amma ba Nakande ba ne ya ba ni ba. Wani ne daga cikin mutum shida da suka je wajen cin abincin Fadila mai suna Sale Kinsa.
“Ba na tunanin wannan kudin aiki ne na farmakin Fadila, ya dai ban kyauta ne saboda muna zuwa gidan Injiniya tare.”
Wani da shi ma yake cikin wadanda ake zargi, Bello Mudassir ya ce, “ni sana’ar hada takalma nake yi, ina shagona Manu Nakande ya zo ya karbi sunana ya ce bayan kwana biyu zai kai sunana wajen Hon Satomi domin in samu tallafin kudi in kara jari.
“Sai ranar Lahadi ya zo a Babur da wasu mutum biyu ya ce in bi su. Da muka isa wajen shakatawa, sai Nakande ya ce mana wannan matar ba ta tare da Satomi, kuma tana cin mutuncinsa.
“Sai ta zagi Nakande shi ma ya zage ta, wanda hakan ya sa muka buge ta. Abin da ya sa muka buge ta shi ne ta zagi Nakande.”
Yadda suka ci mutuncina —Fadila
Da take bayani, Fadila Abubakar ta ce, “ina zaune a shagona kawai sai na ‘yan daba sun zagaye ni suna cewa ogansu ne ya turo su da suka ce za su iya sadaukar da rayuwarsu a kansa.
“Wai ma za su iya kashe ni. Bayan sun doke ni, suka ci min zarafin sannan suka ce in suka dawo za su kashe ni.
“Maganar gaskiya har yanzu ban san me na musu ba, kawai siyasa ce kuma kowa na da ra’ayinsa.
“Ina tunanin an kawo min harin ne saboda na bayyana ra’ayina duk da cewa da farko ba su fada min dalili ba.”
Da take bayani kan bidiyon da ya karade kafafen sadarwa inda take cewa tana karuwa da dan majalisar, sai ta ce, “sun tursasa ni na fadi abubuwa da dama a bidiyon, idan ban fada abin da suka so ba sai suka mare ni, amma maganar gaskiya ban samu komai ba daga wajensa, kawai na yi maganar ce cikin firgici.”
Fadila ta kara da cewa, “ni ba ‘yar siyasa ba ce, kawai ni marubuciya ce kuma ina rubuce-rubucena a shafukana.
“Har yanzu rubuce-rubucena suna nan a shafukana.
“Ina rubuta ra’ayina ne kuma ban ambaci sunan kowa ba, amma sai suka ce dole sai na goge.
Game da ko tana da wata alaka da dan majalisar, sai ta ce, “a baya ina da alaka da shi.
“Har yanzu ba na jin dadi saboda raunuka da na samu. Ina so a kwato min hakkina.”
Ban ji dadin lamarin ba —Injiniya Satomi
A nasa jawabin, Injiniya Satomi Ahmed ya ce bai ji dadin lamarin ba, musamman ganin cewa Mace ce aka ci wa zarafin.
“Ina so a sani cewa ba na goyon bayan cin zarafin mata.
“Ina bakin cikin abin da ya faru da Fadila, kuma ina amfani da wannan damar wajen cire kaina daga wannan lamarin. Ba ni da masaniya a kan wannan lamarin ko kuma irinsa da zai faru a gaba.
“Tuni na umarci jami’an tsaro su gudanar da bincike domin gano bakin zaren lamarin.