Shugaba Bola Tinubu ya ce wadanda suka kashe dakarun soji 16 a yankin Okuoma da ke Karamar Hukumar Ughelli a Jihar Delta, za su ɗanɗana kuɗarsu.
A ranar Alhamis ne wasu bata-gari suka yi wa wasu dakarun soji kisan gilla lokacin da suke kokarin sulhunta rikici tsakanin ƙabilar Okuama da Okoloba a Jihar Delta.
- Yanke Alaƙar Soji: Muna tattaunawa da Nijar — Amurka
- Yadda masu wasa a gidan gala ke nutsuwa a lokacin azumi
Bata-garin sun hallaka Kwamandan soji daya, Manjo biyu, Kyaftin daya, sojoji 12 da kuma wani mutum daya.
Tinubu cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, ya bayyana kisan a matsayin “jahilci” da cewa dole a hukunta wadanda suke da hannu a lamarin.
Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da aka kashe tare da bayyana aniyar gwamnatinsa na hukunta wadanda ke da hannu a kisan sojojin.
Shugaban ya ce, “Wannan lamarin, ya sake nuna irin hatsarin da ma’aikatanmu da mata ke fuskanta a bakin aiki. Ina jinjina wa jarumtarsu da jajircewarsu game da kishin kasa.
“A matsayinmu na al’umma, dole ne mu ci gaba da tunawa da kuma karrama duk wadanda ke bai wa kasarmu kariya. Dakarunmu da suka mutu a yankin Okuama sun bi sahun ‘yan mazan jiya.
“Jami’an sojojinmu su ne jigon kasarmu. Duk wani hari da aka kai musu hari ne kai tsaye ga al’ummarmu. Ba za mu yarda da wannan ɗanyen aiki ba.
“Na bai wa hedikwatar tsaro da babban hafsan soji cikakken ikon gurfanar da duk wanda aka samu da hannu wajen aikata wannan laifi.
“Gwamnatina ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai mun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane yanki na Najeriya.”