Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus ko COVID-19 a Najeriya ya haura 200.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC ce ta sanar da hakan a shafinta Twitter.
“Zuwa karfe 10.30 na daren 3 ga watan Afrilu, akwai mutum 209 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”.
Adadin ya kai haka ne bayan da aka samu sabbin kamuwa mutum 25: “Goma sha daya a Legas, shida a jihar Osun, uku a Yankin Babban Birnin Tarayya, uku a jihar Edo, biyu a jihar Osun, daya a jihar Ondo, daya kuma a jihar Ondo”.
- COVID-19: Yadda doka ta shafi masu kayan abinci a Abuja
- Yar Buhari ta koma cikin danginta bayan kwanaki 14 a killace
Hukumar ta NCDC ta kuma ce an samu karin mutum da suka rasu sakamakon kamuwa da cutar a jihar Edo. Hakan ne ya kawo adadin wadanda suka riga mu gidan gaskiya ta wannan hanya zuwa hudu.
Wadanda suka warke aka sallame su zuwa yanzu sun kai mutum 25.