Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum 11 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.
Wannan ya sa adadin mutanen da zuwa yanzu aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 81.
“Zuwa karfe 11:55 na daren ranar Juma’a 27 ga watan Maris, an tabbatar da karin mutum 11sun kamu da COVID-19”, a cewar sanarwar da hukumar ta NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter.
An dai samu karin mutanen ne a Yankin Legas inda aka sanar da karin mutum takwas; sai kuma jihar Enugu inda aka samu mutum biyu da kuma mutum daya a jihar Edo.
A cikin mutum 81 har yanzu mutum daya ne ya rasa ransa sanadiyyar cutar yayin da aka sallami mutum uku tun bayan barkewar cutar a Najeriya.
11 new cases of #COVID19 have been reported in Nigeria: 8 in Lagos, 2 in Enugu & 1 in Edo State
As at 11:55pm 27th March, there are 81 confirmed cases of #COVID19 reported in Nigeria. 3 have been discharged with 1 death. pic.twitter.com/7p3v3qAcGM
— NCDC (@NCDCgov) March 27, 2020
A cewar hukumar NCDC jihohin su ne:
Lagos- 52
Abuja- 14
Ogun- 3
Ekiti- 1
Oyo- 3
Edo- 2
Bauchi- 2
Osun-1
Rivers-1