Hukumomin lafiya a Najeriya sun bayyana cewa zuwa yanzu mutum 40 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Coronavirus ko COVID-19 a kasar.
Adadin ya karu ne bayan da aka samu wasu mutum hudu da aka tabbatar sun kamu.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta ce biyu daga cikin mutanen sun yi balaguro ne zuwa kasashen waje.
“Zuwa karfe 11.30 na daren 23 ga watan Maris an tabbatar da mutum 40 sun kamu da COVID-19”, a cewar sanarwar da hukumar ta NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter.
- Coronavirus: Zaman zulumi a Bauchi, gwamna ya killace kansa
- Coronavirus: An rufe Masallacin Kasa da ke Abuja
Uku daga cikin sabbin kamuwar a Legas suke, inji hukumar, yayin da daya ke Yankin Babban Birnin Tarayya.
Alkaluman hukumar dai sun nuna cewa 28 daga cikin mutum 40 din da aka tabbatar a Legas suke, bakwai a Yankin Babban Birnin Tarayya, biyu a Ogun. Su kuwa jihohin Edo, da Ekiti, da Oyo suna da mutum guda ko wacce.
Ranar Litinin aka sanar da rasuwar tsohon manajin darakta na Hukumar Kayyade Farashin Man Fetur (PPMC), Sulaiman Achimugu, sakamakon kamuwa da cutar.
Tuni dai gwamnatin Najeriyar ta ba da umarnin takaita hada-hada musamman a biranen Abuja da Legas, sannan ta umarci ma’aikatan da ayyukansu bas u zama dole ba su zauna a gida.