Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 6 da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako karkashin jagorancin Mai shari’a Usman Na’abba, ta dage zaman sauraron shari’ar Abdulmalik Tanko zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu.
Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, kotun dai ta dage sauraron shari’ar ce a sakamakon rashin lauyan da zai kare wadanda ake kara a gaban kotun.
- Yadda ’yan bindiga suka sa garin Kaduna a tsakiya
- Murnar AFCON 2021: Gwamnatin Senegal ta ba da hutun aiki
Ana dai zargin Abdulmalik Tanko da Hashim Isyaku da Fatima Jibril da laifin hada baki wajen kisan yarinyar nan mai shekaru biyar da labarin mutuwarta ya karade duk wano kwararo da sako mai suna Hanifa Abubakar.
Da yake gabatar da kara, Babban Alkali kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan ya bayyana wa kotu cewa sun zo da kararrakin da suke tuhumar wadanda ake zargi suna kuma neman kotu ta ba su dama su karanta.
Sai dai lokacin da kotun ta tuntubi wadanda ake kara ko suna da lauyan da zai kare su, sun sanarwar kotun cewa ba su da shi don haka suna neman gwamnati ta ba su lauyan da zai kare su kamar yadda Kundin Tsarin mulkin kasa ya tanada.
A kan wannan roko ne Alkalin kotun Mai sharia Usman Na’abba ya umarci Gwamnatin Jihar Kano da ta samar wa wadanda ake tuhuma lauyan da zai tsaya musu a shari’ar sannan kuma ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu.
Da yake yi wa Aminiya karin haske, Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan ya bayyana cewa a zama na gaba za su samar wa wadanda ake kara lauya don ganin shari’ar ta tafi yadda ake so.
“Muna sanar da al’umma cewa Ma’aikatar Shari’a a shirye muke game da wannan lamari, mun tanadi shaidunmu don haka ma ba tare da bata lokaci ba a zama na gaba za mu samar wa wadanda ake kara lauyan da zai kare su kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin kasa ya tanada cewa dole ne gwamnati ta sama musu lauya duba da irin girman laifin da ake tuhumar su da aikatawa” inji shi.
Tun makonni biyu da suka gabata ne dai aka gurfanar da Abdulmalik Muhammad Tanko, malamin makarantar da ake tuhuma da garkuwa da kuma kashe dalibarsa ’yar shekara 5, Hanifa Abubakar.
Aminiya ta ruwaito cewa, Abdulmalik ya bayyana gaban kotun ne tare da mutane biyu, Hashimu Isiyaku, da Fatima Jibrin Musa da ake zargi suna da hannu a garkuwa da kuma mutuwar Hanifa.
Mutumin da ake tuhuma dai ya ce da shinkafar bera ta N100 ya yi amfani wajen kasheta.
Wanda ake zargin dai shi ne mai makarantar Noble Kids da ke Kano, kuma ya kashe yarinyar ne bayan ya sace ta, sannan ya yi yunkurin karbar kudin fansa daga iyayenta.
Tun farkon watan Disamban bara ne aka sace Hanifa lokacin da take kan hanyar komawa gida daga makarantar Islamiyya.
Malamin dai ya bukaci a biya shi Naira miliyan shida a matsayin kudin fansarta, inda a wajen karbar kudin ne dubunsa ta cika.
Sai dai ko a lokacin da yake kokarin karbar kudin fansar ma ya riga ya hallaka ta, amma ya ki shaida wa iyayenta.
To sai dai bayan kama shi, wanda ake zargin ya shaida wa ’yan jarida a hedkwatar ’yan sandan Kano cewa da shinkafar bera ta N100 ya yi amfani wajen kashe yarinyar.