✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wacce wainar za a toya tsakanin City da Liverpool?

Liverpool ta yi nasara a wasanni biyu na bayan nan da aka fafata tsakanin kungiyoyin biyu.

A wannan Asabar din Manchester City za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan mako na 29 na Gasar Firimiyar Ingila a Etihad.

City tana ta biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 61, yayin da Liverpool mai maki 42 tana ta shida a teburin.

Wannan shi ne wasa na hudu da za su fuskanci juna a tsakaninsu kuma na biyu a Firimiyar Ingila a bana, bayan da Liverpool ta ci 1-0 ranar 16 ga watan Oktoban 2022.

A cikin jerin wasannin baya bayan nan da aka fafata tsakanin kungiyoyin biyu a kakar wannan wasanni, City ta yi nasara a daya yayin da Liverpool ta yi nasara a biyu.

Magoya bayan Manchester City na fatan Erling Haaland zai buga wasan na hamayya da Liverpool, domin rage tazarar maki tsakani da Arsenal.

Gunners ce ta daya a kan teburi da tazarar maki takwas, kenan City mai rike da kofin bara na fatan hada maki uku a kan Jurgen Klopp, domin kada Arsenal ta bayar da karin tazara mai yawa.

Arsenal wadda saura wasa 10 a gabanta ta karkare kakar bana, na fatan lashe Premier a karon farko tun bayan 2003/04, wadda za ta karbi bakuncin Leeds ranar Asabar.

Haaland, wanda ya ci kwallo 42 a wasa 37 da ya yi wa City na jinya, wanda bai yi atisaye ranar Alhamis ba.

Magoya bayan Arsenal za su yi fatan Haaland kada ya buga wasan, bayan da Phil Foden ke jinya a karawa da Liverpool, wadda ke fatan shiga ’yan hudun teburi, domin buga Gasar Zakarun Turai a badi.

To sai dai cikin wasannin gaba da Arsenal za ta buga za ta ziyarci Anfield ranar 9 ga watan Afirilu da zuwa Etihad ranar 26 ga watan Afrilu, kenan maki shida kenan a kasa.

“Ba za mu iya sauya sakamakon sauran kungiyoyin da za su buga wasanninsu ba, abin da za mu iya shine sa kwazo a dukkan fafatawa da muke fuskanta,” in ji Mikel Arteta.

City tana da kwantan wasa daya, bayan da Manchester United mai kwantai biyu ta uku a teburi, za ta ziyarci Newcastle ranar Lahadi a St James Park.

Tottenham wadda take ta hudun teburi za ta buga wasa karkashin kociyan rikon kwarya, Cristian Stellini, wadda za ta fuskanci Everton ranar Litinin.

Ranar Lahadi Tottenham ta raba gari da Antonio Conte, bayan wata 16 da ya ja ragama.

Kungiyoyi tara ne ke fuskantar barin Firimiyar Ingila a kakar nan, koda yake uku ne ke komawa buga Championship a badi.

Wadda take ta karshe Southampton za ta kara da ta 18 West Ham ranar Lahadi, yayin da ta 19 Bournemouth za ta kece raini da Fulham.

Leicester City wadda take ta 17 a kasan teburi za ta yi wasa da Crystal Palace ta 12 – wadda ta sake daukar koci mai shekara 75, Roy Hodgson, bayan da ta kori Partick Viera.

Karo na biyu kenan da Hodgson zai ja ragamar Palace, domin ya ceto kungiyar daga barin Premier League zuwa Championship.

Palace ce kadai wadda ba ta ci wasa ba a shekarar 2023, wadda ta yi canjaras biyar da rashin nasara bakwai.

Wasannin mako na 29 a gasar Firimiyar Ingila:

Ranar Asabar 1ga watan Afirilu

Manchester City da Liverpool
Arsenal da Leeds United
Crystal Palace da Leicester City
Nottingham Forest da Wolverhampton
Bournemouth da Fulham
Brighton da Brentford
Chelsea da Aston Villa

Ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu

West Ham United da Southampton
Newcastle United da Manchester United

Ranar Litinin 3 ga watan Afirilu

Everton da Tottenham