✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wa’adin Tsofaffin Kudi: Mun zuba ido mu ga yadda CBN zai kare da mutanen karkara —Sarkin Musulmi

Ba a nemi shawarar sarakunan gargajiya ba kan batun sauya fasalin takardun naira.

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce Babban Bankin Najeriya (CBN) bai sanya su cikin masu ruwa da tsaki ba kan batun sauya fasalin takardun kudi, dalilin ke nan da suka zuba ido su ga yadda zai kare da mutanen karkara idan wa’adin karbar tsohuwar naira ya cika.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin Babban Jami’in Gudanarwa na CBN shiyyar Sakkwato, Dahiru Usman hadi da wasu jami’an babban bankin ranar Alhamis a fadarsa.

Abubakar ya ce kamata ya yi a ce CBN din ya sanya dukkanin masu ruwa da tsaki tun a matakin farko na sauya takardun na naira, amma sai ya yi biris da sarakunan gargajiya.

“Akwai mutanen karkarar ma da ba su san an sauya kudin ba kwata-kwata, kuma idan ka ba su sabo ba za su karba ba saboda za su zaci na bogi ne.

“Mu ne muke kusa da su, mu ne kuma ke da hanyoyin isar musu da sakon, don bibiyar kafafen yada labarai ba dabi’ar mutanen karkara ba ce.

“Amma da muka ga ba a saka mu a lamarin ba, sai muka koma gefe mu ga yadda za a kare idan wa’adin karbar tsofaffin kudin ya cika.

“Duk da haka muna rokon CBN ya kara duba wa’adin da ya bayar, domin rashin tsaro na daga cikin dalilan da suka sa mazauna karkara ke tsoron dibar kudi masu yawa su kai bankuna, gudun yi musu fashi a hanya ko ma sace su gaba daya,” in ji shi.

A nasa bangaren, Babban Jami’in na CBN ya ce sun kawo ziyarar ce domin sanar da Sarkin a hukumance cewa an sauya takardun kudin, da kuma neman shawarwarinsa.

Ya kuma yi alkwarin isar da sakon Sarkin ga shalkwatar CBN din da zarar sun kammala zagayen duba yadda bankuna a jihar ke bayar da sababbin takardun kudin da suka je yi.