Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya jadadda cewar ranar 10 ga watan Fabrairu ne wa’adin amfani tsofaffin takardun Naira ya cika.
Emefiele ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da jami’an diflomasiyya a Ma’aikatar Harkokin Waje da ke Abuja a ranar Talata.
- Matawalle ya kori kungiyoyi masu zaman kansu daga Zamfara
- Kotu ta yanke wa malami daurin rai-da-rai kan yi wa yarinya fyade
“Lamarin ya lafa sosai tun bayan lokacin da aka fara biyan kudi a kan kanta wanda hakan ya rage dogayen layuka a ATM.
“Don haka babu bukatar la’akari da wani sauyi daga wa’adin ranar 10 ga Fabrairu,” in ji shi.
Bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rudani game da umarnin kotun kolin wanda ta tsawaita wa’adin zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu, don yanke hukunci kan karar da ke gabanta.
‘Yan Najeriya sun shiga rudani yayin da bankunan kasuwanci suka daina karbar tsoffin takardun tun daga ranar Litinin.
Da yake karin haske, Emefiele ya ce, “Wasu daga cikin shugabanninmu suna siyan sabbin takardun kudi suna ajiyewa saboda wata manufa saboda haka ba zan iya yin karin haske kan hakan ba.”
Emefiele ya ce babban bankin ya san irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke sha sakamakon canjin kudin, amma ya ce tsarin zai iya kawar da kashi 4 cikin 100 na hauhawar farashin kayayyaki.
Ya kuma yi bayanin cewa kamata ya yi a ce adadin kudin da ke zagawa a hannun al’umma ya kai kusan Naira biliyan 700.
Ana iya tuna cewa, a bayan nan ne dai gwamnatocin jihohin Kaduna, Zamfara da Kogi suka maka CBN da Gwamnatin Tarayya a gaban Kotun Koli suna kalubalantar sabon tsarin amfani da sabbin takardun kudi.