Masu sha’awar kwallon kafa sun shafe shekaru goma da suka wuce suna hasashen yadda Cristiano Ronaldo da Lionel Messi za su kare rayuwarsu a harkar wasan kwallon kafa.
Shin manyan abokan gaban biyu za su taba yin wasa tare a kungiya daya? Shin Ronaldo zai koma Manchester United ya yi ritaya a Ingila? Shin Messi zai ci gaba da zama a Barcelona har abada? da dai sauransu.
Yanzu da Ronaldo ya koma kungi Al-Nassr da ke Saudiyya da kuma Messi ya koma Inter Miami da ke Amurka, ’yan wasan biyu sun bar nahiyar Turai, zuwa gasannin da ake ganin ba su da zafi sosai — watakila kuma ba za su kara fuskantar juna a nan kusa ba.
Duk da haka, wani abu daya kowanne daga cikin manyan abokan gaban ke da shi shi ne albashi mai tsoka. Sai dai a abin tambaya shi ne, a cikin su biyun wa zai fi samun kudi?
Ga bayanin albashin Cristiano Ronaldo a Al-Nassr da kuma na Lionel Messi a Inter Miami.
Nawa Lionel Messi zai samu a Inter Miami?
Ficewar Messi daga PSG a karshen kakar wasa ta bana bai zo da ban mamaki ba. Zamansa na shekaru biyu a kungiyar ya taka rawar gani, amma dai ba a cim ma ainihin manufar komawarsa can ba, wato lashe Kofin Zakarun Turai.
Messi ya yana son komawa Barçalona, amma tabon ficewar sa daga Camp Nou a 2021 da kuma rashin tabbacin zuwansa ya sa ya zabi komawa Inter Miami daga PSG, duk da cewa akwai tayi mai tsoka da aka yi na komawa Saudiyya, kasar da yanzu Cristiano Ronaldo ke wasa.
Rahoton na cewa an yi wa Messi tayin albashin Fan miliyan 344 don ya koma kungiyar Al-Hilal a Saudi Arabiya, amma a maimakon haka, ya zabi dan kankanin albashin Fam miliyan 43 a Inter Miami.
Wannan shi ne albashin kulob dinsa, kodayake akwai kulla yarjejeniya da kamfanoni irin su Apple da adidas, wanda zai sa Messi zai samu fiye da Fam miliyan 43 a shekara.
Albashin Ronado a at Al-Nassr?
Sanannen abu ne cewa a harkwar kwallo Saudiyya kasa na da duk irin kudin da ake magana a halin yanzu. Kafin yanzau Gasar Major da ke Amurka ke narka kudi haka harkar, kafin kasar Sin ta karbe ragamar da dan gajeren lokaci.
Amma a halin yanzu Saudiyya ce wurin da taurari irinsu Ronaldo, Karim Benzema da N’Golo Kante za iya karbar duk irin albashi mai tsoka da dan kwallo ke nema.
Messi ya yi wa Ronaldo fintinkau a wajen cin Gasar Cin Kofin Duniya, amma dai a halin yanzu Ronaldo yana iya yi masa fariya game da albashinsa.
Al-Nassr na biyan tsohon dan wasan na Manchester United da Real Madrid da Juventus Fam miliyan 177 a duk kakar wasa.
Kafin komawarsa Saudiyya, albashinsa Fam miliyan 20 a shekara a Man Utd kafin ya koma Juventus ta fara biyan sa Fam miliyan 26 a shekara.
Fam miliyan 177 da ake biyan Ronaldo da Saudiyya ba karamin kudi ba ne, watakila shi ya sa irin su Benzema da Kante suka yanke shawarar komawa Saudiyya domin shiga Gasar Saudi Pro League.
Kafin wani ya yi tunanin Messi ya ci wani irin nasara a nan ta hanyar rashin zuwa Saudiyya, ka tuna cewa shi jakadan kasar ne kuma ana ba shi diyya mai kyau.
Sannan duk da cewa Messi ya sha gaban Ronaldo wajen wasu abubuwa, Ronaldo na zama a Saudiyya ne a matsayin jakada ga kasar, wadda kuma take biyan sa wasu karin kudade masu kauri.
Dangane da kudin da ’yan wasan biyu suke samu a zahiri a kowace shekara, abu ne da ba za a iya fada kai tsaye ba, saboda akwai batun kulla yarjejeniyar talla da dangoginsa, wadanda ba su da iyaka, ga kuma karin wasu hanyoyin samun kudaden shiga.
Amma in dai tsurar albashi ake magana, to abin da Ronaldo ke karba ya fi ninki hudu na albashin Messi.