✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Villarreal ta lashe gasar EUROPA

Karo na farko ke nan da Villarreal ta lashe kofi a tarihinta.

Kungiyar kwallon kafa ta Villarreal ta doke Manchester United a wasan karshe na gasar EUROPA a bugun da kai sai mai tsaron raga.

Villarreal ta fara zura kwallo a minti na 29 ta hannun dan wasanta Gerard Moreno.

Bayan dawowa daga hutun takaitaccen lokaci, Manchester United ta farke kwallon ta hannun Edison Cavani, a minti na 55.

An shafe minti 90 ba tare da wata kungiya ta sake zura kwallo a raga ba, inda alkalin wasa ya busa tashi daga wasan.

Daga bisani aka tafi zagaye na biyu, inda aka buga minti 15 a kowane zagaye.

Daga karshe aka zarce zuwa bugun daga kai sai mai tsaron raga.

’Yan wasan Villarreal gaba daya sun jefa kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga, inda a ’yan wasan Manchester United, mai tsaron ragarta David De Gea ya zubar da bugun.

Villarreal ta yi bugu 11 inda kowane dan wasa ya ci kwallonsa, yayin da kungiyar Manchester United ta yi bugu 11, amma ta ci 10.

Villarreal dai ta zamo zakarar gasar EUROPA ta 2021.

Kocin Villarreal, Une Emery ya sake kafa tarihi a gasar, inda ya zamo ya lashe gasar sau hudu.

Ya taba lashe gasar da kungiyar Sevilla sau uku a jere a shekarar 2014, 2015 da 2016.

Kazalika, wannan shi ne karo na farko da kungiyar ta Villarreal ta taba lashe wata gasa a tarihinta.