✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Venezuela ta sanya dokar kulle na kwana 7

Mutum 113,562 sun harbu da cutar a kasar, inda ta kashe 1,028 daga cikinsu.

Gwamnatin kasar Venezuela ta sanar da sake sanya dokar kulle na kwana bakwai da nufin dakile cutar COVID-19 a kasar.

Mataimakiyar Shugaban Kasar, Delcy Rodriguez, ta sanar cewa dokar za ta fara aiki ne a ranar Litinin, kuma dole ne kowa ya bi matakan kariyar da aka shimfida.

Shugaba Nicolas Maduro, ya ce “Bayan sake bullar COVID-19, dole ne mu kare kanmu da al’ummarmu, don haka an saka dokar kulle daga ranar 4 ga Janairu.”

A ranar Talata Mista Maduro, ya ce gwamnatinsa ta cimma yarjejeniya da kasar Rasha domin ba ta rigakafin COVID-19 miliyan 10, don fara gwaji da shi.

Mutum 113,562 ne ke dauke da cutar ta coronavirus a Venezuela, inda ta kashe 1,028 daga cikinsu.