Wasu alkaluma da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar na nuna cewa cutar COVID-19 ta halaka mutane miliyan 15 a tsakanin shekara ta 2020 da 2021 a fadin duniya.
Alkaluman da hukumar ta fitar ranar Alhamis sun ce adadin ya hada da mutanen da suka mutu sanadiyarta, da kuma marasa lafiya musamman a lokacin kulle.
- Kwalekwale ya nitse da yara 24 masu ‘bukukuwan Sallah’ a Katsina
- ’Yan sanda sun fara neman masu lalata da karnuka a Legas ruwa a jallo
Yanzu haka dai adadin wadanda suka rasu sakamakon cutar sun fi miliyan 6 in ji hukumar.
A don haka ta ce a dage da zuba jari a bangarwn lafiya a fadin duniya saboda kada agajin bada gaggawa ya gagara idan an samu wata annoba irin Corona.
Wata makarantar cibiyar alkaluman lafiya mai suna Health Metrics da ke Amurkan ta fitar da sanarwa makamanciyar ta WHO, da kiyasin mutuwar mutane fiye da miliyan 15.
A hannu guda kuma, hukumar lafiyar ta ce an sami asarar rayuka da dama saboda amfani da ka’idojin cutar.
Makamancin haka ya hada da karancin hadarin mota a tituna da a bakin aiki, saboda mutane na kulle a gida lokacin.