Hukumomin lafiya a China sun sanar da samun mutane dubu 3 da dari 4 da suka harbu da cutar Covid -19 a cikin sa’o’i 24, adadin da ya ninka na ranar Asabar.
Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa wannan lamarin ya tilasta dokokin kulle a yankunan da annobar ta fi shafa, a yayin da kasar ke kokarin yakar matsala mafi rauni a cikin shekaru 2.
- Ronaldo ya kafa tarihin zama dan wasa mafi yawan kwallaye a duniya
- Sojojin Rasha sun harbe dan jaridar Amurka a Ukraine
Wani jami’in ma’aikatar lafiya ya sanar a ranar Lahadi cewa an sanya kwarya kwaryar dokar kulle a birnin Jilin, inda aka hanadaruruwan mutane fita daga gidajensu, a yayin da aka rufe ilahirin birnin Yanjin da ke iyaka da Koriya ta Arewa.
China, inda cutar ta fara bulla a shekarar 2019 ta ci gaba da daukar tsauraran matakai don dakile annobar, inda ta aiwatar da dokokin kulle masu tsauri,da kuma gwaji ba kakkautawa.
Amma bullar nau’in cutar na Omicron a baya bayan nan yana kalubalantar matakan da hukumomi ke dauka.