Gwamnatin kasar Venezuela ta sanar da sake sanya dokar kulle na kwana bakwai da nufin dakile cutar COVID-19 a kasar.
Mataimakiyar Shugaban Kasar, Delcy Rodriguez, ta sanar cewa dokar za ta fara aiki ne a ranar Litinin, kuma dole ne kowa ya bi matakan kariyar da aka shimfida.
- Saudiyya na yi wa mutum 440,000 rigakafin coronavirus kyauta
- ‘Amurka za ta fi kowa cin gajiyar rigakafin coronavirus’
- Tallafin Korona: Trump ya rattaba hannu kan kudirin raba wa Amurkawa Dala tiriliyan 2.3
Shugaba Nicolas Maduro, ya ce “Bayan sake bullar COVID-19, dole ne mu kare kanmu da al’ummarmu, don haka an saka dokar kulle daga ranar 4 ga Janairu.”
A ranar Talata Mista Maduro, ya ce gwamnatinsa ta cimma yarjejeniya da kasar Rasha domin ba ta rigakafin COVID-19 miliyan 10, don fara gwaji da shi.
Mutum 113,562 ne ke dauke da cutar ta coronavirus a Venezuela, inda ta kashe 1,028 daga cikinsu.