✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Van Nistelrooy zai soma aikin horaswa a kaka mai zuwa

Ya rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin horas da kungiyar har zuwa shekarar 2025.

Tsohon dan wasan Manchester United da Netherlands, Ruud van Nistelrooy, zai karbi aikin horas da kungiyar PSV Eindhoven da ke kasarsa Netherlands daga kakar wasa mai zuwa.

Cikin sanrwar da ta fitar a ranar Laraba, kungiyar ta PSV ta ce za ta raba gari da kocinta na yanzu Roger Schmidt a karshen kakar wasa ta bana.

Van Nistelrooy, wanda ya taka leda a PSV tsakanin shekarun 1998 zuwa 2001, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin horas da kungiyar ne har zuwa shekarar 2025.

Ruud van Nistelrooy

Van Nistelrooy, wanda ya yi ritaya daga buga wasa a shekarar 2012, ya zura kwallaye 35 a wasanni 70 da ya buga wa kasarsa ta Netherlands.

Tuni dai tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United ta fitar da wata sanarwa tana taya shi murna tare da yi masa fatan alheri a kan abin da ya sa gaba.