Shahararren dan fim din Amurka Jean Claude ban Damme zai shirya fim din Indiya nan da wata shida.
Ya ce, hakan ne a lokacin taron bikin gasar International Indian Film Academy (IIFA) Awards da aka gudanar a Mumbai da ke Indiya.
“Labari ne na soyayya, da kuma aikatau irin na fina-finan Indiya. Mun kammala shirye-shirye, za mu sanya daya daga cikin fitattun jaruman Indiya. Za mu dauki darakta daga daraktocin Indiya.” Inji ban Damme
Ya ce: “Jaruman Indiya suna matukar kokari, sun fi mayar da hankali wurin al’adarsu da suka hada da rawa da waka da kida kuma hakan na burge ni. Ka ga mutane da yawa na yin abu guda lokacin daya.”
Za a dauki fiye da rabin fim din a tsaunin Himalayas da kuma biranen Indiya “Nan da wata shida za mu fara daukar fim din.” Ya ce daga karshe.
Van damme zai shirya fim din Indiya
Shahararren dan fim din Amurka Jean Claude ban Damme zai shirya fim din Indiya nan da wata shida. Ya ce, hakan ne a lokacin taron…
