✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Valencia ta kori Gennaro Gattuso

Ya zuwa yanzu dai Valencia ba ta sanar da wanda zai maye gurbin Gattuso ba.

Kungiyar Valencia mai buga gasar La Liga a Sifaniya ta sallami kociyanta, Gennaro Gattuso.

A sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Litinin, ta ce ta cimma yarjejeniyar raba gari tsakaninta da kociyan kowa ya kama gabansa.

Wannan hannun riga da aka yi na zuwa ne bayan rashin nasara a hannun Valladolid da ci 1-0 da kungiyar ta yi a ranar Lahadi.

Gattuso ya tafi ya bar kungiyar a mataki na 14 a teburin La Liga da tazarar maki daya tsakaninta da ’yan ukun karshe.

A bana dai, a wasanni biyu kacal Valencia ta iya samun nasara – a gasar Copa del Rey – sai dai tuni Athletic Bilbao ta hankado ta yayin karawar matakin kwata-final da suka yi a makon jiya.

Haka kuma, a Spanish Super Cup, Real Madrid ce ta doke ta a wasan daf da na karshe da ya kai su zuwa bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Gattuso wanda tsohon hazikin dan wasan tsakiya ne, ya ba da gudunmuwar lashe Gasar Kofin Duniya da Italiya ta yi a shekarar 2006.

Gattuso wanda ya lashe Gasar Zakarun Turai sau biyu a AC Milan lokacin yana murza leda, ya jagoranci horas da da kungiyoyin Milan da Napoli duk a Italiya.

Ya zuwa yanzu dai Valencia ba ta sanar da wanda zai maye gurbin Gattuso ba wanda ya koma kungiyar a watan Yunin bara kan yarjejeniyar kaka biyu.

Sai dai ta ce kungiyar za ta ci gaba da harkokin wasanni karkashin kulawar tsohon kociyan rikon kwarya na kungiyar, Voro Gonzalez.