Jam’iyyar APC ta shirya tsaf domin shiga tsakani a rikicin da ke tsakanin ‘ya’yanta na Jihar Kaduna.
Mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi ne ya sanar da hakan inda ya ce jam’iyyar ta kafa wani kwamiti na musamman domin dubi a kan yadda aka samu sabani tsakanin ‘ya’yan nata har ya kai ga rusa gidan Hunkuyi.
An kafa kwamitin ne karkashin shugabancin mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Kudu Segun Oni, sai membobinsa Chief George Moghalu da shugabar matan jam’iyyar Hajiya Rhmatu Aliyu.