Ana zargin wata uwa a jihar Enugu da kashe ’ya’yanta biyu saboda tsananin kuncin rayuwa.
Lamarin ya faru a unguwar Trans Ekulu da ke yankin birnin na Enugu.
- An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano
- Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa
An ga gawarwakin yara biyu a gidan lokacin da jami’an tsaro sukashiga ciki, lamarin da ya tayar da hankulan jama’ar unguwar.
Yaran da ake zargin uwar tasu da kashewa sun hada da yarinya mai suna Esther Arinze mai shekara hudu da haihuwa da kuma kaninta mai suna Chibusoma.
Ana zargin an yi amfani da makami mai kaifin gaske wajen ji wa yaran raunuka a jikunansu kafin su rasu.
Majiyar labarinmu da rundunar ’yan sandan yankin Trans Ekulu sun amsa kiran gaggawar ne daga unguwar aka shaida musu faruwar lamarin inda su kuma ba su yi kasa a gwiwa ba suka rankaya zuwa gidan inda suka iske gawarwakin yara jina-jina.
Daga bisani dai ’yan sanda sun kwashe gawarwakin yaran zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Enugu, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar su.