✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: An ƙaddamar da aikin sabunta ginin Majalisar Dokokin Bauchi

Aikin ya haɗa da inganta kayan aiki, ofisoshi, da kuma gina sabon ofishin hukumar kula da harkokin majalisa.

Gwamna Bala Muhammad ya ƙaddamar da aikin gyare-gyare da sabunta ginin Majalisar Dokokin Bauchi kan kuɗin da ya haura Naira biliyan bakwai, wanda ya haɗa da inganta kayan aiki, ofisoshi, da kuma gina sabon ofishin hukumar kula da harkokin majalisa.

A yayin ƙaddamarwar da aka gudanar ranar Talata, Gwamna Bala ya bayyana cewa wannan gyara na cikin shirin gwamnatinsa na sauya fasalin birane da samar da muhalli mai kyau ga ma’aikata domin sauƙaƙa aikinsu.

Ya ƙara da cewa tuni aka riga aka biya rabin kuɗin aikin domin tabbatar da cewa aikin ya kammala a kan lokaci.

Kwamishinan gidaje da muhalli, Danlami Ahmed Kawule, ya ce aikin zai ƙunshi gyaran zauren majalisar, ofisoshin mambobi, gina sabbin hanyoyin ruwa da wutar lantarki na masu amfani da hasken rana, da kuma gyara titunan cikin majalisar.

Tun da farko, mambobin majalisar sun koma ofishin tsohon mataimakin gwamna domin ci gaba da aikinsu yayin da ake gudanar da gyaran.

Gwamnan ya yaba wa fahimtar da ke tsakaninsa da majalisar, yana mai cewa hakan ne ke bai wa gwamnati damar aiwatar da ayyukan ci gaba.

Kakakin Majalisar, Abubakar Y. Suleiman, ya bayyana godiya bisa wannan ci gaba, yana mai cewa haɗin kai tsakanin majalisar zartarwa da majalisar dokoki na taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba a jihar.