✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Bauchi ya bai wa ɗalibai 4 da suka yi bajinta a JAMB kyautar N4m

Gwamnan ya ce an bai wa ɗaliban kyautar ne domin ƙara musu ƙwarin gwiwa a harkar karatunsu.

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bai wa ɗalibai huɗu ’yan asalin jihar da suka fi cin jarabawar JAMB ta 2024 kyautar kuɗi Naira miliyan huɗu.

Ɗaliban sun haɗa da Kawthar Shehu wadda ta samu maki 348, Geoffrey Yakubu mai maki 347.

Sauran sun haɗa da Abdullahi Garba wanda ya samu maki 347, da kuma Magaji Umar mai maki 333.

Da yake magana lokacin gabatar da kyautar a ranar Talata, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Bauchi, Yahuza Adamu, wanda ya wakilci gwamnan.

Ya ce an bayar da kyautar ne don ƙarfafa wa ɗaliban gwiwa domin su dage wajen samun nasara a karatunsu.