More Podcasts
A duk lokacin da aka ce an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abubuwa na daban da kuma ba su damar shakuwa da ’yan uwa da abokan arziki.
Kamar yadda masana harkar harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da nashi irin matsalolin, ya kuma kamata a ce ana ware wa dalibai wasu lokuta na musamman don samun hutu daga karatun da suka koya.
- NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa
- DAGA LARABA: Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba Buhari
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan abubuwan da ya kamata yara su ringa yi yayin hutun makaranta.
Domin sauke shirin, latsa nan