✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwa ta aurar da ’ya ba tare da sanin mahaifinta ba a Kano

Sai dai malamai sun ce auren bai dauru ba

Wata rikita-rikita ta kunno kai a Jihar Kano bayan da wata mata ta aurar da yarta ba tare da sanin mahaifinta diyar ba, laamarin yake shirin jefa auren cikin rudani.

Lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan mahaifin yarinyar, mai suna Alhaji Muhammad ya saki mahaifiyar yarinyar inda kuma ya gargade ta da kada ta aurar da yarinyar ba tare da izininsa ba.

Sai dai magidancin ya ace abin mamaki kawai sai ya ji labarin an daura auren ’yar tasa, inda ya ce ba zai yardaba har sai an warware auren.

Da yake zantawa da gidan rediyon Freedom da ke Kano, mahaifin yarinyar ya ce ko a baya tsohuwar matar tasa ta yi yunkurin aurar da ’yar tasu ga wani dan uwanta, inda kuma ya ce bai yardaba.

Ya ce daga nan ne kuma sai ba su sake tuntubarsa ba, sai labari ya ji wai an daura wa ’yar tasa aure.

Ko da aka tuntubi dan uwan mahaifiyar amaryar, Baba Hussaini Garko, ya ce shi dai ya san an daura aure, amma ba shi ne ya yi mata Waliyyi ba.

Aure bai dauru ba – Malamai

Sai dai da aka tuntubi wani malamin addinin Musulunci a Jihar ta Kano, Dokta Muhammad Nazifi Inuwa, ya ce ba a daura aure ba tare da iznin mahaifi ba ko kuma wanda ya nada a matsayin Waliyyi a madadinsa.

Malamin ya ce a shari’ance, wannan auren bai dauru ba.

“A addinin Musulunci, ba ya halatta a daura aure ba tare da izinin mahaifin mace ko Waliyyi ba kamar yadda Hadisai suka tabbatar. A don haka, duk macen da ta yi aure ba tare da izinin mahaifinta ko Waliyyi ba, to wannan auren bai dauru ba, babu shi,” inji malamin.